Duniya na ci gaba da la’antar Isra’ila kan mamayar Falasdinawa a Jenin

Ahmed Gheit ya yi kira ga masoya zaman lafiya su sa baki a dakatar da wannan mugun zalunci.

Duniya na ci gaba da la’antar Isra’ila kan mamayar Falasdinawa a Jenin

Harin Isra’ila a Jenen, Falasdinu. Hoto: Aljazeera

Kasashen Larabawa da kuma kungiyoyi da dama a duniya suna ci gaba da la’antar miyagun hare-haren da Isra’ila ta kaddamar a birnin Jenin na Yamma da Kogin Jordan, inda ta kashe akalla mutum 10 tare da raunata sama da 50.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Masar ta la’anci hareharen na Isra’ila “a kan fararen hula da ba su yi laifin komai ba tare da amfani da karfi marar misali,” in ji wata sanarwa da ta fitar.

Jami’an Masar sun yi gargadi kan “mummunan hadarin” da ka iya biyo bayan kai hari ga al’ummar Falasdinu.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Jordan ma ta bukaci kasashen duniya su kawo karshen “Mummunan bala’in da haren-haren Isra’ila a Jenin za su iya jawowa,” in ji wata sanarwa.

Haka kasashen Iran da Turkiyya sun yi kakkausar suka kan hare-haren sojin na Isra’ila a kan Falasdinawa.

Babban Sakataren Kungiyar Kasashen Larabawa, Ahmed Gheit, ya ce “Jefa bama-bamai a birane ta jiragen sama da rusa gidaje da motoci da kuma lalata hanyoyi mummunar daukar fansa ne da ka iya kara tabarbara al’amura.”

Ya yi kira ga masoya zaman lafiya su sa baki a dakatar da wannan mugun zalunci.

Wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya kan Ayyukan Jin-kai a Falasdinu, Lynn Hastings ta ce, “ta kadu” kan munin harin na Isra’ila a Jenin.

Ta fadi a shafinta na Tiwita cewa: “Wajibi ne a bayar da damar isa ga dukkan wadanda aka yi wa rauni.”

Majalisar Hulda ta Musulmi da Amurka wadda ta sha la’antar hare-haren sojin Isra’ila, ta bukaci Amurka ta hana ta’asar sojin Isra’ila a Jenin.

“Gwamnatin Isra’ila ta haukace, saboda ta san babu abin da gwamnatin Biden za ta yi mata,” in ji Babban Daraktan Majalisar, Nihad Awad a wata sanarwa. Ya ce, “Wajibi ne a canja hakan.”

Mahukuntan Falasdinu sun ce kusan Falasdinawa 3,000 ne suka tsere daga gidajensu a Jenin bayan hairn na ɗaruruwan sojin Isra’ila ta sama a yankin a ranar Litinin.

Firayi Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ce za a ci gaba da kai farmakin muddin aka ga bukatar hakan, yana mai cewa farmaki ne na fatatakar ’yan ta’adda.

Wakiliyar BBC ta ce wasu mutane sun shaida mata cewa Isra’ila na tsare da magidanta da ƙananan yara maza a sansanin ’yan gudun hijira na Jenin.

’Yan siyasar Falasdinu sun bayyana yanayin da yunƙurin mamaye gidajensu. Akalla Falasɗinawa 10 aka kashe zuwa Litinin, a cewar hukumomin lafiya a yankin.

Ma’aikatar Lafiya ta Falasɗinu ta ce, an jikkata mutum 50 kuma 10 daga cikinsu sun ji munanan raunuka.

Sojojin Isra’ila sun ce ba su da “nufin’ mamaye sansanin ’yan gudun hijirar na Jenin, ko su zauna a yankin tsawon lokaci,” kamar yadda wani babban hafsan sojin Isra’ila ya bayyana.

Jami’in ya ce sojojin Isra’ila sun shiga sansanin Jenin kuma suna “kai samame ne saboda sahihan bayanan da suka samu” ta hanyar amfani da “dabarun faɗa na musamman” don yaƙi a yankuna masu cinkoso da nufin rage yiwuwar ritsawa da fararen hula.

Jagoran Hamas, Ismail Haniyeh, ya bayyana harin da aka kai wa sansanin da rashin imani kuma babu tausayi.

Yadda gobara ta ƙone kasuwar babura a Zamfara

Mun fara binciken turmutsutsin tallafin abinci — Shugaban ’Yan Sanda

Tinubu ya soke ayyukansa saboda rasuwar mutane a Abuja da Anambra

NNPC ya rage farashin fetur zuwa N899