Duniya na jimamin mutuwar tsohon Sakataren Harkokin Wajen Amurka

Ya taka babbar rawa a fagen diflomasiyya a duniya ta daidaita tsakanin Rasha da China a shekarun 1970,

Duniya na jimamin mutuwar tsohon Sakataren Harkokin Wajen Amurka

Henry Kissinger

Kasashen duniya na jimamin mutuwar tsohon babban jami’in diflomasiyyan Amurka Henry Kissinger wanda ya mutu a ranar Laraba yana da shekaru 100.

A lakacin da yake raye marigayi Henry Kissinger ya rike matsayin sakataren harkokin wajen Amurka a lokacin yakin cacar baka karkashin gwamnatocin Richard Nixon da Gerald Ford tsakanin shekarun 1972 i zuwa 1975.

Shi dai Kassinger dan asalin kasar Jamus ne kuma an haifasa a shekarar 1923 a Bavaria, sai dai ya dauki takardun Amurka bayan ya yi gudun hijira kasar a lokacin da yake da shekaru 20 da haihuwa.

Babbar rawar da ya taka a fagen diflomasiyya a duniya ita ce daidaita tsakanin Rasha da China a shekarun 1970, sai dai kuma juyin mulkin da Amurka ta kitsa a kasar Chile a shekarar 1973 da mamayar Timor ta Arewa a shekarar 1975 da kuma yakin Vietnam sun dakushe tasirinsa a idon duniya.

Sai dai kuma bajitar da ya nuna wajen sasanta rikice-rikice ciki har da jagorantar yarjejeniyar tsagaita buda wuta a Vietnan sun farfado da tauraronsa, lamarin da ya kai shi ga lashe kyautar zaman lafiya ta Nobel a shekarar 1973 wacce ta haifar da cece-kuce.

Henry Kissinger ya cika shekaru 100 a duniya a watan Mayun da ya gabata kuma ziyarsa ta karshe ita ce wadda ya kai kasar China a watan Yulin da ya gabata inda ya gana da shugaba Xi Jinping.

Kasashen duniya na ci gaba da bayyani alhini a game rasuwar tsohon jami’in diflomasiyyan wanda ya taka muhinmiyar rawa a siyasar Amurka da kuma hulda tsakanin kasa da kasa.