Duniya Rumfar Kara
Bahaushe na cewa tsalle daya ake yi a shiga uku, a kuma yi dubu a kasa fita. Wanda duk ya samu kansa a irin wannan matsayin zai kasance cikin gagarumar damuwar da za ta hana shi sukuni, zai kuma yi ta kokarin neman mataimaki, ko wata dabarar ficewa daga cikin irin wannan yanayin. Irin halin […]
Bahaushe na cewa tsalle daya ake yi a shiga uku, a kuma yi dubu a kasa fita. Wanda duk ya samu kansa a irin wannan matsayin zai kasance cikin gagarumar damuwar da za ta hana shi sukuni, zai kuma yi ta kokarin neman mataimaki, ko wata dabarar ficewa daga cikin irin wannan yanayin. Irin halin da tsohuwar Ministar Mai ta kasar nan, Mrs Diezani Allison-Maduekwe ta samu kanta ke nan a halin yanzu, a wata kasa can daban, inda ta taso, ta kuma bude ido, ta kuma nakalci halin rayuwa mai armashi da ban sha’awa, wacce ta dace da ta hamshakan masu kudi, ko manya-manyan ‘ya’yan sarautar da kan je can kasar don holewa.
A yanzu haka ta shiga hannun hukumomin Turawan da ke bincikenta, ba dare, ba rana, don su gano maboyar makudan kudaden haram, na fitar hankali, da ta halasta wa kanta, wadanda ake zargin ta tsibe a wasu bankunan kasar Birtaniyya, inda ta arce tun bayan da aka wancakalar da gwamnatin ubangidanta, Goodluck Jonathan a zaben watan Maris da ya gabata. Hukumomin Birtaniya sun zakulo ta daga makwancinta, tare da wasu mutane hudun da aka ce abokan cin mushenta ne, an kuma fara amshe ‘yan kudaden da aka samu a hannuwanta, an kuma gabatar da ita gaban kotun da ta hanzarta bayar da belinta, daidai da yadda dokar kasar ta kayyade.
Misis Diezani dai ta fara kasaita ne a siyasar Najeriya yayin da Shugaba Umar ‘Yar’adua ya nada ta Ministar Sufuri, bayansa kuma sai dan Jiharsu ta Bayelsa, watau Goodluck Jonathan ya nada ta Ministar albarkatun Man Fetur, inda ta rika kamar danyar kubewa, har ta kai ga matsayin Shugaban kungiyar kasashen Duniya Masu Arzikin Man Fetur, OPEC. A lokacin da take jan zarenta bai tsinke mata ba, ta kuma ci karenta ba babbaka, tana ta cin duniyarta anini-anini abinta, ba wanda ya isa ya daga mata kara, kuma hatta Majalisar kasa ma shakkarta take, ba ta amsa gayyatarta, haka nan ana ji, ana gani, ta gagari kowa.
Duk da cewa talakawa sun kosa su ga an yi hukunci mai gamsarwa game da wadanda ake zargi da daka-wawa bisa dukiyarsu, amma gwamnatin Buhari na bin al’amarin a sannu-a-sannu don a tabbatar an yi abin da ya kamata wajen binciken, ana kuma la’akari da cewa ba a tozarta kowa ba, ana kare hakkin duk wanda aka gayyata yayin da ake tuhumarsa. Shi ya sa ‘yan Najeriya suka kwantar da hankulansu, ganin cewa an dauki hanyar kamanta gaskiya da tsayar da adalci a binciken da ake yi da kuma tsarin hukunta wadanda aka samu da aikata laifi, kuma dangane da haka ne manyan kasashen duniya ke goyon bayan dukkan matakan da Gwamnatin Buhari ke dauka na yaki da ha’inci da rashin aminci.
Yanzu dai mutuncin Diezani ya zube a idanun ‘yan Najeriya da kuma ‘yan wasu kasashen da ke da mua’amala da ita, domin kuwa jama’a na tunanin ta yaya wai za a ce mace kamarta, mai zurfin ilmi, kwararriya a fannonin rayuwa iri-iri, wacce kuma ta gogu a sha’anin mulki da siyasa, har ta samu daukakar da ta kai ta kololuwar matsayi a kasarta za ta biye wa zuciya har ta zarme cikin fariya da dagawar banza? Yaya aka yi har ta kasa gane cewa mutunci ya fi kudi yayin da take tara dukiyar, hakan kuma ya janyo mata asarar mutunci da kuma hana ta jin dadin dukiyar? Wai shin ta manta cewa wanda duk ya dumbuji dukiyar talakawa da sunan sata sai ya kunyata a gaban jama’a?
A’aha, Diezani ta taba tsayawa ta yi tunanin makomarta game da abubuwan da ta aikata, bisa zargin cewa da ita da makararrabanta sun yi ta jidar danyen mai, suna fitarwa ketare, suna samun kudin haram din da suke halastawa? Tana sane kuwa cewa zargin zai bata mata suna, ya kuma janyo wa danginta da abokan huldarta kunyar da za su kasa daurewa? Bar ta wannan! Me mijinta, mutumin da kowa da kowa ya gasgata cewa na kwarai ne, mai gudun abin duniya, zai ce game da wannan sakarcin da ake zargin uwar ‘ya’yansa da aikatawa? Kowa dai ya san cewa mijin Diezani ya bauta wa kasarsa yadda ya kamata, kuma ba a taba gwada mar yatsan zargi ba, domin har Gwamnan mulkin soja ya yi a Jihar Imo, zamanin milkin Buhari.
Wanda duk ya nemi amsoshin wadannan tambayoyin da aka rattaba zai ji takaicin zargin da ake yi wa Diezani na zubar da mutuncinta a banza don taimakon wasu marasa imani da takawa wajen tsiyata kasarta da kuma jefa sauran jama’a cikin kangin talauci da mayata. Amma babban abin takaici game da haka shi ne zubar da mutuncin ‘ya’ya mata, domin kuwa ta kunyata su dangane da wannan kwazon da ake zarginta da aikatawa na caba satar da ‘ya’ya maza ba za su iya tafkawa ba. A yanzu dai an tabbatar da cewa ashe dai da gaske ne ikirarin da mata ke yi na cewa abin da dukkan wani da namiji zai iya yi, mace za ta aikata fiye da haka. Akwai wanda zai musanta wannan batun?
Idan har makudan kudaden da ake zargin Diezani da handamewa da gaske ne, to ba shakka al’ummomin kasar nan za su shiga uku. Idan wata mace guda ce kadai ake zargi da tafka sata irin haka, to ina ga na sauran da ba a rigaya an bankado irin tasu satar ba? Ashe kuwa idan haka ne akwai sauran aiki a gaban Gwamnatin Buhari, kuma wajibi ne a dukufa binciken inda dukiyar kasar nan ta zurare zuwa aljiffan azzaluman da suka kudance da dukiyar haram. Ita kuma Misis Diezani yanzu ne za ta shiga taitayinta, kuma idan zargin da ake yi mata ya tabbata, to za ta san duniya fa rumfar kara ce, domin kuwa ga shi nan ta ruguzo mata, tana cikin sharbar lagwada karkashin inuwarta.