Duniya ta yi Allah-wadai da hukuncin kisan da aka yanke a Masar
kasahen duniya da kuma kungiyoyin kare hakkin bil’adama na ci gaba da yin Allah-wadai da hukuncin kisan da wata kotun Masar ta zartar ga mutane 683 ranar Litinin din da ta gabata.Mutanen ciki har da Shugaban kungiyar ‘Yan uwa Musulmi, Muhammad Badie an tuhumesu ne da goyon bayan gwamnatin tsohon Shugaba Muhammad Morsi da kuma […]

kasahen duniya da kuma kungiyoyin kare hakkin bil’adama na ci gaba da yin Allah-wadai da hukuncin kisan da wata kotun Masar ta zartar ga mutane 683 ranar Litinin din da ta gabata.
Mutanen ciki har da Shugaban kungiyar ‘Yan uwa Musulmi, Muhammad Badie an tuhumesu ne da goyon bayan gwamnatin tsohon Shugaba Muhammad Morsi da kuma mara wa kungiyarsu baya wanda gwamnatin sojin kasar ta dade da bayyana ta da “haramtacciya”. A dokar Masar dai kafin hukuncin ya tabbata akan mutanen, sai ya samu amincewar Shugaban Jami’ar al-Azhar Mufti Shawki Allam.
Jim kadan bayan bayyana hukuncin kotun, arangama ce ta kaure a birnin Alkahira tsakanin magoya bayan kungiyar ta ‘Yan uwa Musulmi da kuma jami’an tsaro. Hakazalika, a Jami’ar al-Azhar ma an samu rawotannin da ke cewa mutane da dama ne suka jikkata bayan da ‘yan sanda sukai kokarin hana wasu dalibai gudanar da wata zanga-zanga.
A wani kokari na kwantar da hankulan ‘yan kasar, babban mai gabatar da kara na Masar, Hesham Barakat ya ce zai daukaka karar hukuncin kisan zuwa kotun gaba. Amma matakinsa bai kwantar da hankulan iyalan wadanda aka yanke wa hukuncin ba.
Wani dan uwan mutanen Amir Isma’il ya ce “kafin yanke hukuncin sai da kotun ta gabatar shafi fiye da 100 na tuhumce-tuhumce da take wa kowane daga cikin mutanen, sai dai kuma kotun ba ta bayyana mana hujjojin da ta dogara da su ba wajen daukar wannan hukuncin.” Inji shi.
Majalisar dinkin Duniya ma, Allah-wadai ta yi da hukuncin inda ta ce ta yi amannar cewa an yanke shi ne ba tare da adalci ba. kungiyar Kare Hakkin Bil’adama ta (Amnesty International) ta bayyana hukuncin ne da wani babban kuskure da ke cike da rashin adalci.