Duniya za ta kasance cikin duhu na mako biyu

Cibiyar Binciken Sararin Samaniya ta NASA da ke kasar Amurka ta ce duniya za ta yi fama da matsanancin duhu na kwanaki 15, wato a tsakanin 15  zuwa 29 ga watan Nuwamban 2015. Cibiyar ta NASA, ta bayyana cewa, al’amarin kan dade bai auku ba, tsawon miliyoyin shekaru.Masanan taurari da ke aiki a NASA sun […]

Duniya za ta kasance cikin duhu na mako biyu
Duniya za ta kasance cikin duhu na mako biyu

Cibiyar Binciken Sararin Samaniya ta NASA da ke kasar Amurka ta ce duniya za ta yi fama da matsanancin duhu na kwanaki 15, wato a tsakanin 15  zuwa 29 ga watan Nuwamban 2015. Cibiyar ta NASA, ta bayyana cewa, al’amarin kan dade bai auku ba, tsawon miliyoyin shekaru.
Masanan taurari da ke aiki a NASA sun yi nuni da cewa, duhun duniyar zai fara a tsakanin karfe  3:00  na dare, a ranar 15, sannan ya kare a ranar 30 ga Nuwamban bana da karfe 4: 15 na safe.
A cewar jami’an hukumar, “Duhun Nuwamban” zai auku ne a sanadiyyar wani karo da  duniyoyin da ke sararin samaniya, wato duniyar benus da ta Jupiter za su yi.
Shugaban Hukumar NASA, wanda Shugaba Obama ya nada, Charles Bolden, ya gabatar da wata makala mai shafi dubu ga fadar mulki ta White House, don gabatar da bayanai kan al’amarin.
A cewar bayanan da ke kunshe cikin rahoton. Ranar 26 ga Oktoban 2015, duniyoyin benus da Jupiter za su kusanci juna, kuma ratar da ke tsakaninsu ba za ta wuce ta digiri daya ba. Duniyar benus za ta taho ta bangaren Kudu maso Yamma da Jupiter, inda za ta haifar wa benus haskawa har sau 10, har ma ta fi duniyar Jupiter haske.
Hasken d ake cikin benus zai kona iskar gas din da ke cikin Jupiter, al’amarin da zai haifar da yamutsi. Wannan yamutsin rugugin iskar gas zai fitar da iskar Hydrogen cikin sararin samaniya, kuma gas din zai hadu da rana da ke haska duniya a daidia karfe 2: 50 na rana.
Yawan iskar hydrogen da ya hadu da rana zai haifar da rugugin da zai fashe, har ya sanya zafin yanayin ya karu da digiri dubu tara na ma’aunin Kelbin nan take. Ita kuwa rana za ta yi kokarin hana wannan karar rugugin fashewar, inda za ta fitar da turirin zafi, wanda zai dusashe launin ranar har ta yi duhu. Wannan al’amari zai dauki rana kimanin mako biyu kafin ta koma yadda take. A lokacin da rana ke yin sanyi, haskenta zai dusashe ya yi duhu.
Wasu sassan duniya za su samu haske na tsawon minti bakwai zuwa takwas, amma daga nan duniyar za ta koma cikin duhu gaba daya har sai yanayinta ya dawo daidai.
A cewar Bolden: “Ba ma sa ran aukuwar wani muhimmin al’amari a lokacin da za a yi fama da duhun. Abin da kawai yanayin zai haifar wa duniya, shi ne, karuwar zafi daga digiri shida zuwa takwas. Babu wanda zai shiga damuwa. Wannan lamari ya yi daidai da yanayin da mutanen Alaska kan samu kansu a lokacin hunturu.”