Duniyar Aljannu (1)
Na dade ina natsari a kan aljannu da kuma duniyarsu.na taba rubutu a wannan mai kanu AL KALAMIN ALJANNU, na jima ina tattaunawa da masana a kan wannan fanni, na kuma sha yin hira da wadanda ke ikirarain suna tare da su; na kuma sha yin gaba da gaba da ’yan buge, wadanda kan shirya […]
Na dade ina natsari a kan aljannu da kuma duniyarsu.na taba rubutu a wannan mai kanu AL KALAMIN ALJANNU, na jima ina tattaunawa da masana a kan wannan fanni, na kuma sha yin hira da wadanda ke ikirarain suna tare da su; na kuma sha yin gaba da gaba da ’yan buge, wadanda kan shirya siddabarun karya su yi ikirarin wai hulda da aljannu suke yi, da kuma wadanda ke zambatar mutane da sunan mutanen boye.
Na ci karo da mata masu karya da na boye, sun ce sun hana su aure, don su sheke ayarsu. Da kishiyoyi masu ikirari da aljannu, don su hana mijinsu zaman lafiya da abokiyar zamansu. Dadewar Da nayi a neman sanin ‘Duniyar Aljannu,’ ta sanya na dan san tsakanin zare da abawa a kan wannan al amari.
Ina abokantaka ta zumunci da wadansu da ke ikirarin cewa, ‘aljannu na zo masu, ko suna shigarsu,’ kuma suna mu’amala da su. wasu gaskiya wasu kuma labari, wasu kawai suna yi ne don tada kura da kuma yin kunnuwan jaki ga kura.
Na samu littafai a kan wannan fanni,don ta kai ga na so fassara wasu labarai ga masu karatunmu daga wasu littafai guda biyu da na karanta. Littafi na farko sunansa TALES OF THE JINN, wanda Dokta Ibrahim Abbasi ya wallafa asalinsa aka rubuta shi da yaren farsi, aka kuma fassaras hi da Larabci, wanda Naser Karimi ya fassara da Ingilishi, kamfanin soft wabe publications da ke kasar Iran suka buga shi.
A shafi na 29 na wannan littafin na ga wani labari mai cike da darasi, wanda na ga kawo wa masu karatunmu zai yi amfanin gaske. Labarin ya faru ne a kasar Masar a shekarar 1980, kuma lokacin da abin ya faru sai da ya dauki hankalin duk duniyar kasashen Larabawa, kafofin watsa labarai a lokacin suka yi ta yayata lamarin.
Wani matashi ne mai suna Abdul’Aziz Muslim Shaheed, wanda ake wa lakabi da Abu Kaf, dan shekaru 33, yana karatu a kwaleji yaki ya barke tsakanin Masar da isra’ila. ya ajiye karatun ya shiga aikin soja. a wajen yakin ya ji ciwo, wanda jin ciwon ya jawo masa shanyewar barayin jiki.
Ya dawo gida wajen mahaifiyarsa da ’yan uwansa ya zauna jinya, aka yi ta magani ciwo ya ki ci, ya ki cinyewa. Wata rana yana kwance a dakinsa sai kawai ya ga wata mata ta keto bango. Ta zo inda yake cikin tsoro da firgici ya kalleta, matar ta tsaya inda yake ta ce masa, “dan samari sunana Haajat. Kuma aljana ce, amma Musulma. Zan iya warkar da wannan ciwon da ke damunka, amma bisa sharadin ka auri diya ta, Haajat ta ce ka yi tunani kafin in sake dawowa.
Tsoro da firgici ya kama Abul Kaf, ya kasa ba ta amsa, kuma ya kasa fadar wa kowa labarin da safiyar daren da abin ya faru. A dare na biyu. Haaj at ta sake dawowa. Ta ce, zan warkar da kai zan kuma taimaki al’ummar Musulmi, domin ni ma musulma ce.
A dare na uku Abul Kaf ya kulle dakinsa, ya dade tagogi, yadda ba wanda zai iya shigowa. Yana kwance sai kawai ya ji Haajat ta kara shigowa. Wannan karon ta zo tare da diyarta. Abu Kaf ya kalli diyar, ya ganta kyakykyawa a fuska, amma jikinta wani iri daban, ya kalli Haajat ya ce ya amince,
Mahaifiyar ta kawo duk kayan biki da na daurin aure, aka yi a cikin daki, aka kuma kawo amaryarsa, duk a cikin dakin yana kwance cikin jinya, bayan amaryarsa ta zo sai yaji wani sanyi a kafarsa, sai kawai ya ji ta mike.
Da safe aka ga ya bude kofa da kansa. Aka ganshi yana tafiya lafiya lau. Gida ya barke da murna da farin ciki. aka yi ta zuwa murna Abul Kaf ya warke. Bayan kwana biyu sai aka ga ya fara wasu halayya. Sai ya kulle dakinsa. Ya yi kwana da kwanaki ba ya fitowa, sai aji yana raha shi daya, sai aka dauka kwanakin da ya yi yana jiya sun sa ya tabu, alhali yana holewa ne da amaryarsa, bayan shekara biyu suka samu yaya biyu.
Bayan wani lokaci aljana Haajat ta sake dawowa ta shaida wa Abu Kaf cewa na yanke shawarar in taimaki mutane ta hanyarka, ta hanyar warkar da su, da ciwuwwuka. Don haka ina son ka samu wani gida ka koma kai kadai inda za ka samu walwala kai da matarka da ’ya’yanku,
Bayan kwana uku Abu kaf ya samu wani gida a wani waje da ake kira Shebr al-Kheyman. A nan ya fara bada maganin cututtuka ga marasa karfi da raunana marasa lafiya, kuma maganin na aiki sosai, ana sha ana warkewa da ya kalli mara lafiya. Sai ya fahimci me ke damunsa da abin da za a yi masa ya warke. Ya rika aikin wasu ya amshi kudi kadan, wasu marasa abin da za su bayar ya yi masu aikin kyauta. Sannu sannu sai ya shahara, aka san shi, kuma aka rikka tururuwa zuwa wajensa, wanda abin da yake yi ya sanya, hukumar da ke sa ido ga masu aikin likita ba bisa ka’ida ba, ta kasar Masar ta kafa wani kwamitin bincike a kansa, a asirce kuma aka tatttara bayanai masu dama a kan aikace-aikacensa. Wanda ya gabatar da binciken wani manjo din soja ne, mai suna Manjo Muhammad Adi al-Talee.
Bayan da aka samu cikakkun hujojji aka nemi Abu kaf ya gurfana gaban kotu. A gaban alkali ya bukaci Abu Kaf ya amsa duk ayyukan da ke zargin yana na bada magani ba tare da iznin hukuma ba, cewa lallai yana yi. Ya bayyana wa kotu cewa, shi ma sanya shi ake yi. Ya ce wadda ke sa shi kuwa ita ce, Haaj at. Alkalin ya umurci Abu Kaf ya bayyana inda wannan mata take, domin ya sanya a je a kamo ta. Abu kaf ya ce ai ba mutum ba ce, aljana ce, Musulma. Nan da nan alkalin ya ce wannan zancen banza ne. kuma ya ba da umurnin a je a tsare Abu Kaf tsawon kwana hudu, yana zartar da wannan hukunci wani ciwon kai mai tsanani ya samu alkalin.