Duniyar Aljannu (2)
A ranar biyar ga watan Afrilu. 1980. aka gabatar da Abu Kaff a wata kotu da ke Shebr al-Kheyman, karkashin alkali Rafat Ukashah. A kotun Abu Kaf ya tabbatar da duk zargin da ake yi masa ba tare da ya musanta komai ba. Alkalin ya tambaye shi ko yana iya gano cutar da ke damunsu […]
A ranar biyar ga watan Afrilu. 1980. aka gabatar da Abu Kaff a wata kotu da ke Shebr al-Kheyman, karkashin alkali Rafat Ukashah. A kotun Abu Kaf ya tabbatar da duk zargin da ake yi masa ba tare da ya musanta komai ba. Alkalin ya tambaye shi ko yana iya gano cutar da ke damunsu ya yi musu magani? Abu Kaf ya ce kwarai ko. A take ya yi, masu taimaka wa alkali nazarin cutar da ke damunsu kuma ya yi musu magani, ya kuma yi wa alkalin kansa,
Kotun ta barke da ALLAHU AKBAR. Gardama ta sarke tsakanin Abu kaf da mai gabatar da kara, alkalin ya rasa wani hukunci zai dauka? Sai ya yanke hukuncin akai Abu Kaf zuwa gidan masu fama da cutar kwakwalwa.
A ranar 22 ga watan Afrilu. 1980. Babbar jaridar kasar Masar mai suna al-Jumhuriyya ta buga labari da wata irin muhawara akan lamarin. Likitoci masana, da malaman addini suka yi ta tsokaci da sanya albarkacin baki akan al’amarin. Amma duk a muhawarar ba wanda ya iya bada amsar ya ake yake
iya gano cutar mutum kuma ya bashi magani a kuma warke?
A ranar 22 ga Afrilu 1980. Aka sake kawo Abu Kaf a kotu. Alkali Rafat Ukasha, ya yi hukuncin cewa, kotu ba inda ta samu Abu kaf da laifi. Alkalin ya yi muhawarar cewa, bincike ya tabbatar da cewa Abu Kaf na abin da yake yi ne bisa tilas,kuma ba yadda ya iya dole ne ya yi abin da ake bukatarsa. Alkalin ya ce kotu kuma tabbatar da cewa duk hukuncin da yake badawa na likitanci gaskiya ne. Kuma ba wani abin da yake wanda yake cutar da mutane. A kan haka alkalin ya yanke hukuncin cewa, babu wani laifi da Abu Kaf ya yi, don haka a sallame shi, a kuma kyale shi, ba wata hujja da za a iya kama shi da laifi.
Ana yanke hukuncin Abu Kaf ya yi wata irin hailala da karfin gaske, ya shaida wa ’yan jarida cewa, a lokacin yanke hukuncin Hajaat tana cikin kotun kuma daidai lokacin da alkalin zai fara karanta hukuncinsa. tana tsaye a bayansa, har ya gama karantawa. Da ’yan jarida suka tambaye shi sunanta da kamannuta Abu Kaf sai ya bada amsar cewa, iyakar abin da zan iya fada ke nan a kanta.
A shafi na 24. An kawo labarin wani malami da lamarin ya faru a 1995, mai suna Abbas, wanda wata aljana ta nemi rokon ya aure ta, ita kuma za ta warware duk matsalar samun abin duniya. Abbas ya ce matar ta yi ta zuwa wajensa, tana rokon cewa ya aure ta, ta gan shi, kuma ta ji tana sonsa, ta yi masa alkawarin yalwal arziki da farin ciki aljanar ta yi ta zuwa wajensa yana kin amincewa a haduwarsu na karshe da ita.
Sai ya fusata ya kai mata mari wanda ita kuma ta kawo masa bugu ya shiga yana yin rashin lafiya, wanda yayi ta wahala bai warke ba. Har sai da Allah ya ba shi ikon ziyarar kabarin Imam Rezah[a.s] sannan ya samu lafiya.
A kuma shafi na 27 na littafin ya kawo labarin , wani mutum da aljanna ta aure shi, ya samu wadata, amma ya koma bai iya bukatar sauran matansa. Wannan yasa ya ji tsoron cewa in ya rusa auren da wannan matar, rayuwarsa da dukiyarsa na iya shiga garari.
Wannan yasa ya je wajen wani malami bawan Allah mabiyin Ahlili baiti.[as]mai suna Shek Jafar. Malamin ya ba mutumin wasu wasiku guda biyu daya ya ce ya ba ta, guda kuma ya sanya a kayan da ta kawo masa. Mutumin yayi duk abin da malamin ya ce masa. Aljanar ta shaida masa cewa ba don wadannan wasikun ba, da na kasheka, na kuma lalata dukiyar da na ba ka.
A shafi na 88 na littafin ya kawo labarin da ya faru a birni Tabriz kasar Iran, inda wasu matasan aljannu suka rika ladabar da duk wanda ya yi wasa da ranakun bukukuwa da na makoki a tarihin ahlili bait.
Labaran da aka kawo a wannan littafi suna da yawa, shi ya sa ma har aka yi gargadin cewa kar ka karanta littafin idan shekarunka ba su kai goma sha bakwai ba.
A littafin Wahid Abdussallam Bali, wanda Haythan Kreidly ya fassara daga Larabci zuwa Ingilishii, Kamfanin Darul Kotub al ilimiyya Lebanon suka buga shi. Littafin mai suna da turanci. THE CUTTING EDGE .HOW TO FACE THE EbIL SORCERER. NA larabcinsa kuma sunansa AL SARIM AL BATTAR .FI AL TASSADI LIL SAHARA AL ASHRAR.
A Cikin wannan littafin ya kawo yadda ake kulumboto ana kiran mugun aljani, kuma a sanya shi ya yi wani mugun aiki, kamar haddasa gaba tsakanin masu zaman lafiya. da dai sauran miyagun ayyuka marasa amfani.
A wasu shafukan ya yi bayani hatta halayyar bakake da fararen aljannu. Duniya Aljannu wata duniya mai zaman kanta wanda jahilcinta kansa wasu su rika karya suna ci da gumin aljannu. Wanda wani rubutun da zan kara shi ne taken masu karya da kuma ci da gumin aljjanu.
Danjuma Katsina. Dan jarida ne dake zaune a Katsina.email [email protected] 080359044