Durkushewar Arewa: Da sake

Na san  wasu daga cikin dimbin matsalolin da ke addabar mu a kauyukanmu, musamman a yankunan mu na Hausawa, a takaice Arewa. Za ka ga mutane suna noma suna da kuddi, amma suna barin ‘’ya’yansu tsirara ba sutura, ba ilmi, suna barin iyalansu da ciwo har su mutu a gida, ba su iya cire kudin  […]

Durkushewar Arewa: Da sake
Durkushewar Arewa: Da sake

Na san  wasu daga cikin dimbin matsalolin da ke addabar mu a kauyukanmu, musamman a yankunan mu na Hausawa, a takaice Arewa. Za ka ga mutane suna noma suna da kuddi, amma suna barin ‘’ya’yansu tsirara ba sutura, ba ilmi, suna barin iyalansu da ciwo har su mutu a gida, ba su iya cire kudin  kai su asibiti. Suna tara mata babu kulawa, babu muhalli mai kyau, za ka ga yaro dan kasa da shekara 30 da mata hudu, ’ya’ya birjik, amma ba zai iya biya musu bukatun rayuwa ba.
Idan ka fito ka fadi wata illa akan haka sai al’umma su rabe da addini, su ce kai mai ra’ayin Yahudawa ne, kana so ne ka hana tara zuri’a da yawa. Bayan kuma irin zuri’a da al’ummar mu suke tarawa a yau, ba zuri’a ba ce da za a yi alfahari da ita ba ce ta fuskar zaman lafiya ko dogaro da kai, a’a zuri’a ce, wadda ba za mu taba kaiwa ga ci da irin ta.  Ai ga irinta nan, gamu da yawan zuri’ar, Lallai mun cimma burinmu, mun fi kowace kabila yawa a kasar nan, amma me yawan na mu ya amfanar mana? Duk da yawan na mu mu ne a baya ta bangaren ilimi, mu ne a baya kullum wajen ayyukan tallafa wa juna, mu ne baya ta fuskar jami’an tsaro, ta fuskar likitoci, ta fuskar malamai, ta fuskar lauyoyi, ta fuskar masana’antu da sha’anin banki.
Mu ne baya ta fuskar mulki da ma’aikata a guraben gwamnati, kuma idan ba mu dawo mun zama masu kishin kai ta wajen ba yaran mu ilimin addini da na zamani mai kyau ba, idan ba mu dawo mun rungumi junanmu a matsayin uwa daya uba daya ba, idan ba mu kawar da bambancin akida ba, wata rana sai an wayi gari wasu kananan kabilu wadanda ba su fi cikin cokali ba,idan aka kwatanta su da mu, sai sun dawo sune suke fifiko a kan mu ta kowace fuska, ba tare da mun iya cewa komai ba muna kwance… (kamar yadda muka fara gani).
Babu wata kabila ko wata al’umma da za ta ci gaba akan irin wannan turbar da muka hau.
Mu je mu ga yadda matasa suke taka rawar gani a duk sha’anin da ya shafi ci gaban al’ummarsu, a wasu yankuna na kasar nan. Idan wani mai kudi zai gina kamfani a garinsu, bai isa yasa ko bulo daya a kasa ba sai sun yi yarjejeniya a gina musu makarantu da hanyoyi, kuma zai dauki nauyin karatun ’ya’yansu. Idan za a gina banki a garin su, dole a dauki ma’aikata mafi yawa daga cikinsu. Amma wadanne matasa suke iya bugun kirji a cikin matasan da ke yankunanmu na nan Arewa su yi wa al’ummar su wannan namijin kokarin? Wane banki ka taba ji ya zo wani gari ko wani kauye a yankunan mu ya saurari muryar matasa ko al’umma? Suna zuwa ne su yi abin da suke so, saboda sun san ba mu da wadatattun matasa masu karatu da suka san ’yancinsu wadanda suka san muhimmancin al’ummarsu, wadanda suke da hasashe mai kyau akan abin da suke so su cimma wata rana wanda zai amfani kannensu ko ’ya’yansu.
A nan Arewa akwai muggan masu kudin da ana kallon su suna sayen kamfanoni sun rufewa, a dalilin haka matasa dubu nawa suka rasa ayyukan yi? barayi nawa suka karu? Wa ya san koma bayan da hakan yake jawowa? Mun taba cusa wa matasa irin wannan masaniya sun farga da abin da yake faruwa sun fito sun nuna rashin amincewar su? Ana ta bata tunanin mu wajen nuna mana hanyoyin rayuwa na da can…tsofaffin hanyoyin gudanar da al’amuran rayuwa wadanda sun daina aiki a wannan zamanin. Haka ake so mu ci gaba da rayuwa? Haka ake so mu zama kananan kabilu suna mulkarmu? Ina neman afuwar wadanda wannan rubutun zai bakanta wa rai, saboda ba zan iya shiru ina kallon rugujewar kasar nan, ba tare da na yi magana ba. Da fatan za a dube shi da idon basira.
Bashar Bello Linguist,Sokoto Cinema Jahar Sakkwato. 07063691636.

Matsalar Tsaro: Dole mu faɗakar da mutane yadda za su kare kansu – ACF

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna