Ebola: An daure mutum 6 a Guinea don sun dauki gawa
A ranar Litinin da ta gabata ne aka tsare wasu mutum shida a kasar Guinea bayan sun dauki wata gawar wani dan uwansu a mota, wanda ake zargin ya mutu ne sanadiyyar cutar Ebola. Mahukuntan kasar sun bayyana cewa an zaunar da gawar ne a tsakanin mutum biyu a cikin motar tasi kamar mai rai, […]
A ranar Litinin da ta gabata ne aka tsare wasu mutum shida a kasar Guinea bayan sun dauki wata gawar wani dan uwansu a mota, wanda ake zargin ya mutu ne sanadiyyar cutar Ebola.
Mahukuntan kasar sun bayyana cewa an zaunar da gawar ne a tsakanin mutum biyu a cikin motar tasi kamar mai rai, sanye da riga da wando da kuma tabarau. Har ila yau, sun ce idan bayan kwana 21 suka cika mutanen ba su nuna alamar kamuwa da kwayar cutar ba, za a gurfanar da su a gaban kuliya kan laifin saba dokar kiyaye annobar Ebola. An dai kama mutanen ne a wani shingen bincike, inda wasu jami’an tsaro suka saka ayar tambaya akan gawar saboda yadda suka ba ta motsi, inji sanarwar.
A duk lokacin da aka samu asarar rai sakamakon cutar a kasar, ana bai wa kungiyar agaji ta Red Cross ne domin ta binne gawar, amma iyalai da dama suna bijirewa saboda sun fi so su yi hakan da kansu.
kasar Guinea dai tana kokarin kawo kan yaduwar annobar, wadda ta yi ajalin mutune akalla mutum 2,500 ta kasar tun bayan barkewar annobar a yankin Yammacin Afirka fiye da shekara guda da ta wuce.
Wakilin BBC a babban birnin kasar, Conakry ya ce kwana tara da suka wuce, mutum tara ne kawai a duka fadin kasar suke fama da cutar kuma suna karbar kulawa daga cibiyoyin kula da masu fama da cutar, amma a yanzu haka adadin masu fama da ita ya kusan mutum 30.