Ebola: An tsaurara matakan bayar da biza ga ’yan Najeriya

*Gwamnati ta ce ba ta yarda ba A sakamakon bullar da cutar Ebola ta yi a kasar nan, yanzu ’yan Najeriya suna fustakantar matsala wajen samun biza domin zuwa wadansu kasashe, inda wadansu ofisoshin jakandanci ke matsawa sai an gwada jinin mutum an tabbatar bai kamu da cutar ba kafin a yi masa bizar.A halin […]

Ebola: An tsaurara matakan bayar da biza ga ’yan Najeriya

*Gwamnati ta ce ba ta yarda ba

A sakamakon bullar da cutar Ebola ta yi a kasar nan, yanzu ’yan Najeriya suna fustakantar matsala wajen samun biza domin zuwa wadansu kasashe, inda wadansu ofisoshin jakandanci ke matsawa sai an gwada jinin mutum an tabbatar bai kamu da cutar ba kafin a yi masa bizar.
A halin yanzu dai wadansu kasashe sun sanya Najeriya a cikin kasashen da za su sanya wa ido, wanda hakan ya sanya kasashe irin su Turkiya da Pakistan da Taiwan suka tsaurara matakan bayar da biza ga ’yan Najeriya masu bukatar zuwa kasashensu.
Sai dai gwamnatin tarayya ta ce ba za yarda da wannan matakin da ofisoshin jakandancin suka dauka ba, domin kuwa a ka’idar hukumar lafiya ta duniya (WHO) ba kowane mutum ne ake tantancewa ba, wanda ya yi mu’amala da mai cutar ne kawai ake gwada shi domin a tabbatar bai kamu da cutar ba.
Darektan yaki da cututtuka a kasar nan, Farfesa Abdulsalam Nasidi ne ya tabbatar da haka a Abuja, inda ya kara da cewa, gwamnatin tarayya tuni ta tuntubi wadannan ofisoshin jakandancin da suka tsaurara matakan bayar da bizar.
Farfesa Abdulsalam Nasidi ya ci gaba da cewa ga dukkan alamu  za a iya magance matsalar cutar Ebola daga nan zuwa ranar 6 ga watan Satumbar  nan, lokacin da za a sallami duk wadanda aka kebe ana duba su saboda cudanya da suka yi da Patrick Sawyer, mutumin da ya shigo da cutar kasar nan daga Liberiya, “Mun kama hanyar kore cutar daga kasar nan a halin yanzu,’’ inji shi.
Ya kara da cewa, “Ina tabbatar  muku da cewa, idan har aka ci gaba da kokarin da ake yi a halin yanzu na yaki da cutar Ebola, za a magance matsalar  daga nan zuwa ranar 6 ga watan Satumba. Amma wannan ba ya yana nufin cutar ta tafi gaba daya ke nan, ba za a ta iya sake kunno kai a kasar nan ba.”
Farfesa Sunday Omilabu, wanda wani kwararren likita ne daga asibitin koyarwa na Jami’ar Legas da ya jagoranci likitocin da suka binciki Patrick Sawyer har suka gano cewa yana fama da cutar Ebola, ya ce abin da ’yan Najeriya suke bukatar kulawa da shi sosai a halin yanzu shi ne tsabta. “A rika wanke hannu da sabulu koyaushe; a tsabtace wurin zama da kuma kiyaye cudanya da wanda ke fama da cutar ko kuma duk abin da ya taba. Idan aka kula da wadannan abubuwan za su taimaka wajen kariya daga cutar.’’ Inji shi.
Tsohon Jakadan Najeriya a kasar  Sudan Suleiman dahiru ya bayyana wa Aminiya cewa, lallai  bullar cutar Ebola a Najeriya za ta shafi ’yan Najeriya masu fita daga kasar nan a lokacin da suka sauka a kasar da suka tafi bayan an ba su biza.
Gwamnatin Tarayya dai ta ce mutum daya ne kawai ya rage mai dauke da cutar Ebola a Najeriya, inda a yanzu aka sallami daya daga cikin mutanen biyu da aka kwantar a Jihar Legas sakamakon kamuwa da cutar Ebola da suka yi. A halin yanzu dai daya ne kawai aka kebe don ci gaba da lura da shi.
 Ministan Lafiya Onyebuchi Chukwu ne ya bayyana hakan a lokacin da yake yi wa ’yan jarida karin bayani a kan cutar Ebola a Legas, inda ya ce a yanzu mutane bakwai ne suka warke bayan kamuwa da cutar a Najeriya.
Ya ce tuni aka sallami mutane 129 da aka kebe su tsawon kwanaki 21 bayan an tabbatar ba sa dauke da cutar.
“A cikin mutanen da muka kebe don gano ko suna dauke da cutar, mutum daya ne kawai yake nuna alamomin kamuwa da cutar, har yanzu muna kan bincike, ba mu kai ga fitar da sakamakon binciken ba. Sauran mutanen da muka kebe tsawon kwana 21 ba sa dauke da alamomin kamuwa da cutar.”
Ya tabbatar da mutanen da suka mutu a kasar nan sakamakon cutar har yanzu biyar ne, ciki har da Patrick Sawyer wanda ya shigo da cutar kwanaki 41 da suka wuce.
“An sallami biyu daga cikin masu dauke da cutar, wato likita da kuma wata jami’ar jinya a ranar Talata, wadannan malaman lafiya su ne suka hada jiki da marigayi Sawyer, a yanzu sun cika dukkan ka’idojin da za a sallame su. Kuma an sallame su.
“A yanzu da nake muku karin bayani, mutum daya ne kawai yake dauke da cutar a duk fadin Najeriya, wanda shi ma ya hada jiki da marigayi Sawyer. Wannan kuma alama ce da ke nuna Najeriya ta yi kokari wajen dakile yaduwar cutar.” Inji shi.
A dangane da Naira biliyan 1.9 da Shugaba Goodluck Jonathan ya bayar don a yaki cutar a lokacin da ya sanya dokar ta-baci kan cutar kuwa, sai ministan lafiyar ya ce, wannan kudin ba wai kawai don a yaki cutar Ebola ba ne, a’a, don a inganta harkar lafiya a kasar nan ne.
“Mun ce Naira biliyan 1.9 da shugaban kasa ya ba wa ma’aikatar lafiya ta tarayya, ya bayar ne bisa ga kasafin kudin da ma’aikatar ta tura masa, ba wai an bayar da wannan kudin ne don yaki da cutar Ebola ba.
“Ina kara nanatawa, domin na ji a wadansu wurare har ma a kauyuka, inda dagatai suke tambayar a ba su kasonsu daga cikin kudin. Abin takaici shi ne, koyaushe a Najeriya ana tunanin rabon kudi ne, to wannan kudin ma’aikatar lafiya ta tarayya ne. Za a yi amfani da kudin don samar da kayan aiki ne, wanda a yanzu an riga an ba da umarni kawo su. Za a yi amfani da kudin wajen samar da na’aurorin da za a rika riga-kafi da su, za a samar da magungunan da za rika ba marasa lafiya, za a kuma samar da tantunan da za a rika kebe wadanda suka kamu da cutar.”