Ebola: Ana binciken gida-gida a Saliyo

An fara bincike gida-gida a kasar Saliyo don kakkabe cutar Ebola da ta addabi kasar.Za a gudanar da bincike a gida-gida ne na tsawon wata daya, inda za a fara da Freetown babban birnin kasar. Shugaban kasar Ernest Bai Koroma ya ce za a dakatar da kasuwar ranar Lahadi, sannan za a rage tafiye-tafiye da […]

Ebola: Ana binciken gida-gida a Saliyo
Ebola: Ana binciken gida-gida a Saliyo

An fara bincike gida-gida a kasar Saliyo don kakkabe cutar Ebola da ta addabi kasar.
Za a gudanar da bincike a gida-gida ne na tsawon wata daya, inda za a fara da Freetown babban birnin kasar.
Shugaban kasar Ernest Bai Koroma ya ce za a dakatar da kasuwar ranar Lahadi, sannan za a rage tafiye-tafiye da zirga-zirga jama’a.
Wannan matakin na daya daga cikin matakan da Saliyo ta dauka don kawar da cutar daga kasar, inda a baya gwamnatin kasar ta hana jama’a yin bakukuwa ciki har da na Kirsimeti da Sabuwar shekara.
kasar Saliyo tana daya daga cikin kasashen da suke fama da cutar Ebola, cutar da ta kashe fiye da mutane 6,800 cikin wannan shekarar.
 A wata sanarwar da Shugaba Koroma ya fitar ya ce, bincike gida-gidan ya zama dole ne, wanda yin hakan zai sanya a ga bayan cutar gaba daya a kasar.
Ya ce babu mai boye cuta sai jahili, inda ya bukaci mutane su bada hadin kai a lokacin da aka zo bincike a gidajensu.
Baya ga hana zuwa kasuwar ranar Lahadi, an bukaci a rage lokacin sayayya a ranar Asabar da Lahadi.
Birnin Freetown shi ne yake dauke kashe 50 cikin 100 na mutanen da suka kamu da cutar Ebola a kasar.
Wakilin BBC a kasar Saliyo Umaru Fofana ya ce duk da wannan dokar har yanzu jama’a suna atisaye da kuma taruwa a gabar teku a kasar.