Ebola: Ana tsangwamar bakaken fata a Amurka

Bakaken fata a kasar Amurka sun koka da yadda ake tsangwamarsu tun bayan da aka samu barkewar cutar Ebola a kasar. Lamarin ya yi kamari ne tun bayan mutuwar dan kasar Laberiyan nan Thomas Eric Duncan a birnin Dallas da ke Jihar Tedas a Amurka, a farkon watan nan, bayan ya kamu da cutar, hakan […]

Ebola: Ana tsangwamar bakaken fata a Amurka
Ebola: Ana tsangwamar bakaken fata a Amurka

Bakaken fata a kasar Amurka sun koka da yadda ake tsangwamarsu tun bayan da aka samu barkewar cutar Ebola a kasar.

Lamarin ya yi kamari ne tun bayan mutuwar dan kasar Laberiyan nan Thomas Eric Duncan a birnin Dallas da ke Jihar Tedas a Amurka, a farkon watan nan, bayan ya kamu da cutar, hakan ya sa ana ci gaba da tsangwamar mutanen da suka fito daga kasashen Afirka mazauna a Amurka.
Wakiliyar BBC Leslie Goffe da ke birnin New York ta ruwaito cewa lamarin ya kai ga har ana haramtawa wasu ‘yan Afirka zuwa wuraren aiki tare da kyamar su a wasu wurare da jama’a kan taru don yin mu’amala yau da kullum.
Cutar Ebola ta kashe mutane sama da 4,500 a tsakanin kasashen Laberiya da Guinea da Saliyo da kuma Najeriya wadda a ranar Litinin da ta gabata Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana cewa ta shawo kan annobar.