Ebola: Fiye da mutum 1,000 sun kamu yayin da mamata suka kai 254 a Congo
Akasari waɗanda suke kamuwa da cutar sun fi yawa a lardin Ituri da ke arewa maso gabashin ƙasar Congo.
Adadin mutanen da suka kamu da cutar Ebola a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo ya haura 1,000 kamar yadda alƙaluman mahukunta suka tabbatar a ranar Litinin.
Cibiyar Kula da Lafiyar Jama’a ta Ƙasa (INSP) ta tabbatar da cewa an samu mutum 1,003 da suka kamu da cutar, yayin da adadin waɗanda suka mutu ya kai 254, lamarin da ya nuna kaso 25 cikin 100 na masu kamuwa da cutar na mutuwa.
- Amurka ta ɗage wa Iran takunkumin sayar da mai
- Katsinawa da suka kammala digiri da daraja ta farko za su samu aiki kai tsaye — Radda
Akasarin waɗanda suke kamuwa da cutar wadda aka ayyana ɓarkewar ta a hukumance ne a ranar 15 ga watan Mayu, sun fi yawa a lardin Ituri da ke arewa maso gabashin ƙasar, yankin da ke fama da rikice-rikicen tsaro da hare-haren ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai.
Baya ga Ituri, cutar ta bazu zuwa lardunan arewaci da kudancin Kivu, inda ake ƙiyasta mutane kusan miliyan 15 ke zaune.
Haka kuma cutar ta tsallaka zuwa maƙwabciyar ƙasar Uganda, inda Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce an tabbatar da mutum 20 da suka kamu da ita, yayin da mutum biyu suka mutu.
Sai dai gwamnatin Uganda ta bayyana a farkon watan nan cewa za ta iya shawo kan lamarin.
Masana sun ce ɓarkewar cutar a wannan karon ta samo asali ne daga ƙwayar cutar Bundibugyo, wani nau’i cutar Ebola wanda har yanzu babu rigakafi ko takamaiman maganin da aka amince da shi domin yaƙi da ita.
Rigakafin Ebola da aka samar tsakanin shekarun 2018 da 2019 na aiki ne kawai kan nau’in Zaire, wadda aka sha fama da ita a shekarun baya.
Hukumar Lafiya ta Duniya ta ayyana lamarin a barazanar lafiya ta duniya, tana mai gargaɗin cewa ɓarkewar cutar na iya ɗaukar watanni kafin a samu nasarar shawo kanta.