Ebola: Laberiya ta saka dokar hana fita

A shekaranjiya Laraba ne gwamnatin Laberiya ta kafa dokar hana zirga-zirga inda jami’an tsaro suka killace babban birnin kasar, Monrobia a wani mataki na shawo kan bazuwar cutar Ebola.Shugabar kasar Ellen Johnson Sirleaf ce ta bayana hakan ta wata sanarwar  wadda ta bayyana cewa dokar za ta yi aiki ne  a ciki da wajen yankin […]

Ebola: Laberiya ta saka dokar hana fita
Ebola: Laberiya ta saka dokar hana fita

A shekaranjiya Laraba ne gwamnatin Laberiya ta kafa dokar hana zirga-zirga inda jami’an tsaro suka killace babban birnin kasar, Monrobia a wani mataki na shawo kan bazuwar cutar Ebola.
Shugabar kasar Ellen Johnson Sirleaf ce ta bayana hakan ta wata sanarwar  wadda ta bayyana cewa dokar za ta yi aiki ne  a ciki da wajen yankin yammacin birnin. Idan ba a manta ba a yankin ne aka kai hari a wata cibiyar kiwon lafiya a karshen makon jiya inda maharan suka yi awon gaba da majiyyata cutar  su 17.
Har ila yau,’yan sanda sun harba hayaki mai sa hawaye don tarwatsa dandazon masu zanga-zanga bisa adawa da kakaba masu dokar hana fita.
Shaidu sun ce mazauna yankin a fusace na jifa da duwatsu kan jami’an tsaro da aka jibge don tabbatar aikin da dokar hana zirga-zirga. Kodayake duka wadannan matakan na zuwa ne mako biyu bayan ayyana dokar ta-baci a duk fadin kasar.