Ebola: Ma’aikatan lafiya 75 sun kamu, 17 sun mutu a Kongo — WHO

WHO ta ce akwai yiwuwar cutar ta fara yaɗuwa tun kafin a sanar da ɓullarta a hukumance ranar 15 ga watan Mayu.

Ebola: Ma’aikatan lafiya 75 sun kamu, 17 sun mutu a Kongo — WHO

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana cewa aƙalla jami’an lafiya 75 sun kamu da cutar Ebola, yayin da 17 daga cikinsu suka rasu tun bayan ɓullar cutar a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo.

Daraktar Sashen Ba da Agajin Gaggawa na WHO, Marie Roseline Belizaire, ta ce akwai yiwuwar cutar ta fara yaɗuwa tun kafin a sanar da ɓullarta a hukumance ranar 15 ga watan Mayu.

A cewarta, hakan na nuna cewa wasu daga cikin jami’an lafiya sun kamu da cutar ne kafin hukumomi su gano ɓarkewar ta.

Ta ce ma’aikatan lafiya na ci gaba da fuskantar ƙalubale sakamakon ƙarancin kayan kariya da suka haɗa da safar hannu da takunkumin fuska, waɗanda suke da matuƙar muhimmanci wajen kare su daga kamuwa da cutar.

Sai dai ta bayyana cewa ƙasashe irin su China da Uganda na ci gaba da bayar da tallafi da taimako domin taimakawa wajen daƙile yaɗuwar cutar.

Marie Roseline Belizaire ta kuma jaddada cewa Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo na fama da ƙarancin ma’aikatan kiwon lafiya idan aka kwatanta da yawan al’ummar ƙasar, lamarin da ke ƙara musu wahala a yaƙi da annobar.

WHO ta ce tana ci gaba da aiki tare da gwamnatin Kongo da sauran abokan hulɗa domin shawo kan ɓarkewar cutar da kuma kare lafiyar jama’a.