Ebola na barazana ga Ilimi a Afirka
Wata kungiyar kasa da kasa mai kamun kafa kan habaka ci gaban ilimi tabukaci makarantu a kasashen yammacin Afirka, yankin da cutar Ebola ta fi kamari, su hanzarta bukewa domin ba da damar yara miliyan biyar ci gaba da harkokin karatunsu . A cewarta akwai bukatar samar da wani shirin ilimi na gaggawa ya zuwa […]
Wata kungiyar kasa da kasa mai kamun kafa kan habaka ci gaban ilimi tabukaci makarantu a kasashen yammacin Afirka, yankin da cutar Ebola ta fi kamari, su hanzarta bukewa domin ba da damar yara miliyan biyar ci gaba da harkokin karatunsu .
A cewarta akwai bukatar samar da wani shirin ilimi na gaggawa ya zuwa lokacin da za’a sake bude dukkanin makarantu cikin cikakkiyar kariya.
Ta ce idan ba an dauki managarcin mataki ba, mai yiwuwa yara da dama ba za su sami damar komawa makaranta ba har abada.
Daga cikin wadanda suka goyi bayan wannan kira har da hamshakin attajirin da ya fi kowa kudi a nahiyar Afirka, Alhaji Aliko dangote da jakadan musamman na majalisar dinkin duniya kan harkar Ilimi kuma tsohon Firaministan Biritaniya Gordon Brown.
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce wannan ce annobar Ebola mafi muni a tarihi, inda mutum 5,459 suka rasa rayukansu cikin mutum 15,351 da suka harbu da kwayar cutar a kasashe takwas kafin ranar 18 ga wannan watan. Kuma kasashen da annobar tafi kamari su ne Guinea da Saliyo da Laberiya.