Ebola ta bulla a Amurka a karon farko

Ma’aikatar Lafiya ta kasar Amurka ta bayyana cewa an samu wani mutum da kwayar cutar Ebola a kasar a karon farko, kuma yana samun kulawa a wani asibitin birnin Dallas da ke Jihar Tedas.Mahukunta sun ce mutumin wanda ba a bayyana sunansa ba, an kebe shi kuma Cibiyar Kula da Kiyaye Yaduwar Cututtuka (CDC) ta […]

Ebola ta bulla a Amurka a karon farko
Ebola ta bulla a Amurka a karon farko

Ma’aikatar Lafiya ta kasar Amurka ta bayyana cewa an samu wani mutum da kwayar cutar Ebola a kasar a karon farko, kuma yana samun kulawa a wani asibitin birnin Dallas da ke Jihar Tedas.
Mahukunta sun ce mutumin wanda ba a bayyana sunansa ba, an kebe shi kuma Cibiyar Kula da Kiyaye Yaduwar Cututtuka (CDC) ta ba likitoci da ma’aikatan jinya da kuma marasa lafiya tabbacin cewa za ta shawo kan al’amarin.
Wani jami’in gwamnatin kasar ya ce mara lafiyan dan asalin kasar Laberiya, an kwantar da shi a wani asibiti ranar Lahadin da ta gabata, kamar yadda kafar yada labarai ta Al Jazeera ta ruwaito.
Daraktan Cibiyar CDC Thomas Frieden ya kira wani taron manema labarai  a hedkwatan cibiyar da ke Atlanta, ranar Talata, inda ya bayyana cewa: “Mutumin da ke dauke da cutar ya zo ne daga Laberiya ranar 19 ga watan jiya kuma ya fara bayyana alamomin cutar ne bayan kwana biyar da isowarsa nan. Bayan kwana biyu da bayyanar alamomin ne ya fara neman magani, kuma ranar Lahadin da ta gabata aka kwantar da shi a wani asibiti da ke Jihar Tedas.”
Jami’an asibitin sun bayyana cewa alamomin suna nuni da cewa mutumin yana dauke da cutar Ebola. Cutar ta yi ajalin fiye da mutum 3,000 a yankin Yammacin Afirka kuma ciki harda wasu Amurkawa masu yawa da suka ziyarci yankin. Amma a baya kasar ta yi nasarar warkar da wasu ma’aikatan lafiyar kasar biyu da suka harbu da cutar bayan da aka  mayar da su gida.