Ebola ta bulla a Nahiyar Turai

Ana ci gaba da gudanar da binciken kimiyya a wani asibiti da ke Madrid, babban birnin kasar Spain bayan da wata ma’aikaciyar jinya ta kamu da cutar Ebola a karon farko a kasar, wanda kuma wannan shi ne karon farko da annobar ta bulla nahiyar Turai.Ana kyautata zaton cewa ma’aikaciyar jinyar ta harbu da cutar […]

Ebola ta bulla a Nahiyar Turai
Ebola ta bulla a Nahiyar Turai

Ana ci gaba da gudanar da binciken kimiyya a wani asibiti da ke Madrid, babban birnin kasar Spain bayan da wata ma’aikaciyar jinya ta kamu da cutar Ebola a karon farko a kasar, wanda kuma wannan shi ne karon farko da annobar ta bulla nahiyar Turai.
Ana kyautata zaton cewa ma’aikaciyar jinyar ta harbu da cutar ne bayan ta bai wa wasu ’yan kasar kulawa wadanda cutar ta yi ajalinsu, jim kadan bayan mayar da su gida daga yankin Yammacin Afirka. Har ila yau, akwai wasu mutum uku ciki har da mijin ma’aikaciyar jinyar da a halin yanzu aka killace su.
Hakazalika, Hukumar Tarayyar Turai ta bukaci kasar Spain da ta yi mata bayani kan yadda ma’aikaciyar jinyar ta kamu da cutar. Kodayake, a shekaranjiya Laraba, jami’ai a kasar sun bayyana cewa akwai yiwuwar mata ta kamu da cutar bayan ta taba fuskarta lokacin da take sanya da rigar kariya daga cutar bayan ta duba daya daga cikin mutanen da ke fama da cutar.
Har ila yau, a shekaranjiya Laraba ne aka bayyana mutumin farko da ya harbu da cutar  a kasar Amurka, Thomas Eric Duncan, ya rasu. A bangare  guda kuma mahukunta na ci gaba da sanya ido ga mutanen da marigayin ya yi mu’amala da su.
Fiye da mutum 3,400 ne suka rasa rayukansu tun bayan barkewar annobar a watan Fabrairun bana a yankin Yammacin Afirka.