Ebola ta ci gaba da yaduwa a Amurka

An samu rahoton karin mutum na biyu da ya harbu da cutar Ebola a birnin Tedas na kasar Amurka kamar yadda jami’an kiwon lafiyar kasar suka bayyana shekaranjiya Laraba. Duka mutanen biyu da suka kamu da cutar sun duba marigayi Thomas Duncan, wanda ya rasu a makon jiya bayan ya zama mutum na farko da […]

Ebola ta ci gaba da yaduwa a Amurka
Ebola ta ci gaba da yaduwa a Amurka

An samu rahoton karin mutum na biyu da ya harbu da cutar Ebola a birnin Tedas na kasar Amurka kamar yadda jami’an kiwon lafiyar kasar suka bayyana shekaranjiya Laraba.

Duka mutanen biyu da suka kamu da cutar sun duba marigayi Thomas Duncan, wanda ya rasu a makon jiya bayan ya zama mutum na farko da ya kamu da cutar a cikin kasar. Kodayake, shugaban kwamitin yaki da cutar na Majalisar dinkin Duniya ya ce duniya ta gaza wajen kawo karshen bazuwar kwayar cutar. Hakazalika, Shugaban Amurka Barack Obama ya ce kokarin da duniya take yi don shawo kan cutar Ebola, “bai wadatar ba.”
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana cewa kawo yanzu mutum 4,447 ne suka rasa rayukansu tun bayan barkewar annobar a yankin Yammacin Afirka. Kuma kasashen Saliyo da Laberiya da kuma Guinea su ne annobar tafi kamari.