Ebola ta jawo yajin cin abinci a Guinea

A ranar Talatar da ta gabata ne a wani kauye da ke kasar Guinea aka fara yajin cin abinci saboda matakin gwamnatin kasar na aike wa da sojoji zuwa can. Akalla jagororin kauyen 20 ne a yanzu suke zaman dirshen a gaban majalisar dokokin kasar tun bayan fara yajin cin abincin. Jagoran ’yan adawar kasar […]

Ebola ta jawo yajin cin abinci a Guinea
Ebola ta jawo yajin cin abinci a Guinea

A ranar Talatar da ta gabata ne a wani kauye da ke kasar Guinea aka fara yajin cin abinci saboda matakin gwamnatin kasar na aike wa da sojoji zuwa can.

Akalla jagororin kauyen 20 ne a yanzu suke zaman dirshen a gaban majalisar dokokin kasar tun bayan fara yajin cin abincin. Jagoran ’yan adawar kasar ya ce mamayar da sojojin suka yi wa kauyen mai suna Wome, ya tilasta wa mazauna kauyen mutum 6,000 kauracewa muhallansu. Kodayake ba a samu martani daga gwamnatin kasar ko kuma rundunar sojin kasar ba tukuna. Shugaban Jam’iyyar adawa ta Liberal Party Faya Millimono ya bayyana sashen harshen Faransanci na BBC cewa ya shiga yajin cin abincin saboda nuna goyon bayansa ga jama’ar kauyen.
Har ila yau, a cikin watan Satumban da ya wuce ne gwamnatin kasar ta zargi jama’ar kauyen da hannu a kisan wasu mutum takwas wadanda suke aikin wayar wa da jama’a kai kan annobar Ebola. Sai dai ba a iya fahimtar dalilin kisan mutanen ba, amma an kashe su ne a lokacin da al’ummonin yankin suke musanta kasancewar cutar Ebola da kuma zargin ma’aikatan lafiya da yada kwayar cutar.
A cikin watan Maris din da ya gabata ne aka fara tabbatar da bullar annobar a kasar ta Guinea, wadda daga bisani ta yadu zuwa kasashen Laberiya da Saliyo masu makwabtaka da Guinea. Kuma cutar ta yi sanadiyyar mutuwar fiye da mutum 5,000 a yankin, a cewar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO).