Ebola ta kara bulla a Laberiya

A ranar Talatar da ta gabata ne gwamnatin kasar Laberiya ta tabbatar da cewa wani matashi dan shekara 17, ya rasu sakamakon kamuwa da kwayar cutar Ebola, kuma ba a gano yadda ya kamu da ita ba, da kuma wadanda ya yi mu’amala da su. A yanzu cutar ta kama mutane biyu a kauyen Nedowein […]

Ebola ta kara bulla a Laberiya
Ebola ta kara bulla a Laberiya

A ranar Talatar da ta gabata ne gwamnatin kasar Laberiya ta tabbatar da cewa wani matashi dan shekara 17, ya rasu sakamakon kamuwa da kwayar cutar Ebola, kuma ba a gano yadda ya kamu da ita ba, da kuma wadanda ya yi mu’amala da su.

A yanzu cutar ta kama mutane biyu a kauyen Nedowein inda matashin ya rasu. Hakan yana zuwa ne kimanin mako bakwai bayan an ayyana Laberiya a matsayin wadda ba ta da sauran mai dauke da kwayar cutar.
Hukumomin lafiya sun ce wadanda suka kamu da cutar sun yi ma’amala da matashin ciki hadda wani mai maganin gargajiya.
Fiye da mutum dubu 11 ne suka rasu sakamakon annobar Ebolar tun karshen shekarar 2013. Cutar ta fi hallaka mutane da dama a kasashe Saliyo da Guinea da kuma Laberiya, wadanda suke yankin Yammacin Afirka.