Ebola ta kawo wa sana’ar fawa cikas – danlami Maitsire
Wani matashin mahauci mai kimanin shekara 30 da ke sayar da tsire a Unguwar Obalende a Jihar Legas mai suna danlami Maitsire ya ce cutar Ebola da ta bayyana a kasar nan ta kawo wa sana’ar fawa da sayar da nama cikas a kasar nan.Malam danlami Maitsire ya bayyana haka ne a lokacin da yake […]
Wani matashin mahauci mai kimanin shekara 30 da ke sayar da tsire a Unguwar Obalende a Jihar Legas mai suna danlami Maitsire ya ce cutar Ebola da ta bayyana a kasar nan ta kawo wa sana’ar fawa da sayar da nama cikas a kasar nan.
Malam danlami Maitsire ya bayyana haka ne a lokacin da yake tattaunawa da Aminiya a Legas, inda ya ce, suna fuskantar kalubale a sana’arsu ta sayar da nama a halin yanzu. “Gaskiya kalubalen da muke fuskanta a wannan sana’ar musamman a halin yanzu shi ne na batun cutar Ebola wadda ta kawo wa kasuwarmu tsaiko kwarai da gaske.”
Sai dai duka da haka ya ce shi da sana’ar tsire mutu-ka-raba domin ba abin da zai ce ga wannan sana’a sai godiya ga Allah da rokon Ya ci gaba da ba shi budi, saboda ya ga fa’idar da ke tattare da wannan sana’a.
danlami Maitsire ya ce sama da shekara 10 ke nan da ya fara wannan sana’a da jarinsa, amma tun yana karami yake tare da mahaifinsa yana wannan sana’ar, kuma a wajensa ne ya koya ga shi ya shekara sama da 10 na yi shi kadai.
Da ya koma kan irin alfanun da ke tattare da sana’ar sai Malam danlami ya ce a ciki yake ci yake sha, ya yi sutura ya ciyar da iyalansa har ma ya taimaka wa wasu, gwargwadon hali.
Ya ce zai yi kokarin ganin ’ya’yansa sun yi karatun addini da na zamani, amma bayan sun kammala idan suka ce sana’ar nama za su zai kara musu kwarin gwiwa kamar yadda mahaifinsa ya yi masa.
“Idan na ga wani ya ce zai shiga wannan sana’a idan ya koya ya iya zan kara masa kwarin gwiwa ya yi, domin akwai amfani,” inji shi. Sai dai ya ce idan mutum bai san sirrinm sana’ar ba ya fada cikinta da rana tsaka duk abin da ya same shi, to shi ya jiwo.
Malam danlami ya ce sana’ar tsire ba ta bukatar jari mai yawa, domin da Naira dubu 10 zuwa 20 ya ishi mutum jari a Legas.