Ebola ta tilasta dage ranar komawa makaranta
Sakamakon barazanar da cutar Ebola ke haifarwa Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta ba da sanarwar dage ranar komawa makarantu ga daliban makarantu firamare da sakandare na gwamnati da masu zaman kansu a kasa baki daya.Yanzu daliban wadannan makarantu za su koma makaranta ne a ranar 13 ga watan Oktoba mai zuwa.Ma’aikatar Ilimin ta ce ta […]
Sakamakon barazanar da cutar Ebola ke haifarwa Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta ba da sanarwar dage ranar komawa makarantu ga daliban makarantu firamare da sakandare na gwamnati da masu zaman kansu a kasa baki daya.
Yanzu daliban wadannan makarantu za su koma makaranta ne a ranar 13 ga watan Oktoba mai zuwa.
Ma’aikatar Ilimin ta ce ta yi haka ne saboda daukar matakan kariya game da cutar Ebola.
Kuma daukar wannan mataki ya biyo bayan ganawar da Ministan Ilimi Malam Ibrahim Shekarau ya yi da kwamishinonin ilimi na jihohi a farkon wannan mako a Abuja.
daukar wannan mataki ya zo ne a daidai lokacin da Ministan Lafiya Dokta Onyebuchi Chukwu ya bayyana wa ’yan Najeriya cewa a yanzu mutum daya ne kacal ya rage da kwayar cutar a kasar nan a cibiyar killace masu dauke da cutar Ebola bayan da aka sallami wasu daga cikin wadanda suka warke daga cutar.
Dokta Onyebuchi Chukwu ya bayyana haka ne bayan da ya sanar da sallamar mutum biyu da suka warke daga cutar.
A cewarsa, mutum 13 ne suka kamu da cutar Ebola a Najeriya, ciki har da dan kasar Liberiya, Patrick Sawyer wanda ya shigo da cutar cikin kasar nan a ranar 20 ga Yuli kuma ya rasu bayan kwana biyar.
Dokta Chukwu ya kara da cewa a yanzu mutum bakwai ne suka warke daga cutar a yayin da cutar ta hallaka mutum biyar a kasar nan.
Ya ce, “Ina tabbatar wa ’yan Najeriya da sauran kasashen duniya cewa gwamnati za ta ci gaba da kasancewa a fadake kuma ba za ta yi kasa a gwiwa ba, wajen ci gaba da yin aiki da abokan hadin gwiwarta don tabbatar da an kawar da cutar daga cikin kasar nan.”
Cutar Ebola ta kashe mutum 1,400 a kasashen Guinea da Liberiya da kuma Saliyo.