Ebola: Tsakanin ilimi da siyasa
A farkon wannan mako ne mahukuntan Najeriya a bangaren ilimi suka bayar da umarnin a cfi gaba da rufe makarantun firamare da sakandare na kasar nan, a matsayin bin umarnin Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan kan a guji haduwar jama’a domin kauce wa yaduwar hatsabibiyar cutar nan Ebola.Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta umarci makarantun gwamnati […]
A farkon wannan mako ne mahukuntan Najeriya a bangaren ilimi suka bayar da umarnin a cfi gaba da rufe makarantun firamare da sakandare na kasar nan, a matsayin bin umarnin Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan kan a guji haduwar jama’a domin kauce wa yaduwar hatsabibiyar cutar nan Ebola.
Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta umarci makarantun gwamnati da masu zaman kansu su ci gaba da kasancewa a rufe har zuwa 13 ga Oktoba, “Dukkan makarantun firamare da sakandare na gwamnati da masu zaman kansu, su ci gaba da kasancewa a rufe sai ranar Litinin 13 ga Oktoba, 2014,” inji Ministan Ilimi Malam Ibrahim Shekarau bayan ganawa da kwamishinonin ilimi na jihohi 36.
Ya kara da cewa, “An yi haka ne domin a dauki dukkan matakan da suka dace kafin daliban su koma.”
Minista Shekarau ya ce, taron ya amince ma’aikatun ilimi na jihohi su shirya horarwa kan kiwon lafiya akalla ga ma’aikata bibbiya a makarantun gwamnati da na masu zaman kansu, domin su san yadda za su kula da cutar Ebola, kuma wajibi ne a gudanar da horon nan da 15 ga Satumba.
Kuma Ministan ya bayar da umarnin dakatar da karatun bazara da wasu makarantu masu zaman kasu suke gudanarwa, sannan ya shawarci manyan cibiyoyin ilimi su dakatar da musayar ma’aikata da dalibai da ziyara da zuwa tarurrukan bita a kasashen waje zuwa wani lokaci. Kuma su rika sanya ido kan kara-kainar daliban kasashen waje a harabobinsu da sauran matakai masu dama.
Hakika duk wanda ya saurari wannan mataki da gwamnati ta dauka, zai yi murna cewa gwamnati ta yunkuro domin magance yaduwar wannan muguwar cuta da ta daga hankali jama’a. Kuma abin farin ciki wannan mataki ya zo ne a daidai lokacin da Ministan Lafiya Dokta Onyebuchi Chukwu ya bayyana wa ’yan Najeriya cewa a yanzu mutum daya ne kacal ya rage da kwayar cutar a kasar nan da ke killace a cibiyar killace masu dauke da cutar Ebola.
Sai dai abin bakin ciki da mamaki, a daidai lokacin da gwamnati ta mataki na rufe makarantu, sai ga shi wata kungiyar nema wa Shugaba Jonathan goyon baya mai suna Jakadiyar Sake Fasalin Najeriya, wato Transformation Ambassador of Nigeria (TAN), tana ta gudanar da gangamin goyon bayan Shugaban kasar, ta fara da na Awka ranar 16 ga Agusta wuni biyu bayan samun labarin wata nas da ke karkashin kula saboda cutar Ebola ta gudu daga Legas zuwa Enugu mai nisan kilomita 78 zuwa Akwa. Wannan na nuna rashin girmama wannan umarni na Shugaba Jonathan na a guji taron jama’a don kauce wa yaduwar Ebola.
Sannan bayan mako daya a ranar 23 ga Agusta, TAN ta gudanar da gangamin Kudu maso Yamma a Ibadan mai nisan kilomita 136 daga Legas inda jami’an lafiya ke kokarin gano wadanda Patrick Sawyer da ya shigo da cutar ya yi hulda da su don dakile yaduwarta..
Kuma kungiyar TAN ta fara gudanar da wannan gangami ne mako daya bayan Shugaban kasa ya bayar da wancan umarni.
Kuma kungiyar TAN ta ce za ta yi gangamin shiyyar Kudu maso Kudu a Fatakwal ta Jihar Ribas a gobe Asabar; sannan ranar 13 ga Satumba za ta gudanar da na shiyyar Arewa ta Tsakiya, a Minna ta Jihar Neja; yayin da za ta gudanar da na Arewa maso Gabas a Gombe bayan kwana uku, sai kuma na Arewa maso Yamma a Kano, garin Ministan Ilimin a ranar 27 ga Satumba, wanda shi ne gangami na karshe. Ke nan kungiyar TAN za ta kammala gangamin shiyya-shiyya mako biyu kafin bude makarantun. Kuma har zuwa shekaranjiya Laraba, kwana daya bayan umarnin ci gaba da rufe makarantun, babu alamar masu shirya gangamin za su dakatar da gangamin.
Babban abin tambaya shi ne a tsakanin gangamin siyasa da haduwa a makaranta wanne ne ya fi zama hadari wajen yada cutar Ebola?
Kuma abin mamaki a daidai lokacin da gwamnati ta kyale TAN tana gudanar da gangamin siyasa, sai ga shi ta yi yunkurin hana taron kungiyar lauyoyi ta kasa da aka shirya gudanarwa a wannan mako a Owerri ta jihar Imo.
Hatta tarurrukan addini sai da Shugaba Jonathan ya nemi a rage, haka tarurrukan iyali da na kungiyoyi da sauransu, har zuwa wani lokaci.
Kuma a shekaranjiya Ministan Labarai Mista Labaran Maku, ya fadi a karshen taron Majalisar zartarwa cewa an dage bikin Osun Osogbo da ya kamata a gudanar a gobe, da sauran bukukuwa domin dakile yaduwar cutar.
Abin da ke faruwa yana da daure kai matuka, lamarin da ya sa nake tambayar kaina, any aba gwamnati ta hana komawa makaranta ba ne, domin yin amfani da daliban makarantun wajen halartar gangamin kungiyar TAN don nuna wa duniya tana da magoya baya ba?
Shin me zai hana jama’a su rika zargin cewa ita kanta cutar an sanya siyasa a cikinta, tunda ga shi ba a hana taron goyon bayan Shugaban kasa ba, amma an hana karatu da sauran tarurruka a sassan kasar nan?
Wani abin da ke kara nuna cewa akwai siyasa a cikin lamarin Ebola shi ne yadda kudin da aka ware Naira biliyan daya da miliyan 900 domin yaki da cutar kiri-kiri ana kokarin karkatar da su domin sayen motoci da wasu kayayyaki ga ma’aikata lafiya.
Mistan Lafiya Dokta Onyebuchi Chukwu, ya shaida wa manema labarai cewa kudin Shugaban kasa ya ba ma’aikatar lafiya ce don sayo karin motoci da kuma sayen magunguna da aka riga aka yi odarsu da sauran kayayyaki. Kuma ya ce duk da duniya tana fuskantar hadarin Ebola, ma’aikatarsa a shirye take ta fuskanci duk wata barazanar barkewar cutar.
A gaskiya wannan ya sa nake ganin cewa siyasa musamman nema wa Shugaban kasa ya fi ilimi muhimmanci a wurin shugabannin kasar nan, shi ya sa suka ce a ci gaba da rufe makarantu har zuwa watan jibi, amma suka bari ana gangamin siyasa da ake zagaya sassan kasar nan. Sun yi haka ne saboda ’ya’yansu ba a kasar nan suke karatu ba. Kuma wannan abin bakin ciki ne ganin kwanan nan malaman kwalejojin kimiyya da kere-kere suka janye yajin wata bakwai da suka yi.