Ebola za ta kawo cikas ga yaki da maleriya
Wata babbar cibiya da ke yaki da cutar maleriya mai suna Roll Back Malaria (RBM) Partnership ta ce kokarinta na takaita yaduwar cutar a bana, na iya fuskar cikas saboda annobar Ebola. Shugabar Cibiyar Dokta Fatoumata Nafo-Traoré ce ta bayyana hakan bayan wata ziyara da ta kai yankin Yammacin Afirka, inda ta ce: “Abin da […]
Wata babbar cibiya da ke yaki da cutar maleriya mai suna Roll Back Malaria (RBM) Partnership ta ce kokarinta na takaita yaduwar cutar a bana, na iya fuskar cikas saboda annobar Ebola.
Shugabar Cibiyar Dokta Fatoumata Nafo-Traoré ce ta bayyana hakan bayan wata ziyara da ta kai yankin Yammacin Afirka, inda ta ce: “Abin da na fahimta shi ne hankulan ma’aikatan lafiya ya ta’allaka ne ga cutar Ebola kadai.”
Ta ce bangarorin asibitoci da a kodayaushe suke cike da kananan yara, ya fara zama “kufai saboda karancin ma’aikatan jinya. Mun damu matuka saboda cutar Ebola za ta iya haifar da cikas ga yaki da cutar maleriya”, kamar yadda ta bayyana.
A shekarar 2012, cutar maleriya ta yi ajalin fiye da mutum 7,000 a kasashe ukun da annobar Ebola tafi kamari.
Ta kara da cewa a yanzu kasashen uku suna yaki ne da kwayar cutar Ebola “tsoron shi ne nasarar da aka samu kan maleriya na iya samun koma-baya saboda annobar. Idan aka ci gaba da mayar da hankali ga cutar Ebola kadai, to hakan na nufin za a kara samun mutanen da za su mutu daga cutar maleriya,” inji ta.
Dokta Nafo-Traoré ta ce yawancin wadanda ke fama da zazzabi suna kauracewa asibitoci saboda tsoron kada a killace su a cibiyoyin kebe masu dauke da cutar Ebola. Wata masalar kuma ita ce yadda alamomin farko na kamu da cutar Ebola suke kama da na maleriya.