ECOWAS ta bai wa Sojin Nijar wa’adin mayar da Bazoum kan mulki

ECOWAS ta bai wa sojojin Nijar wa’adin kwana bakwai.

ECOWAS ta bai wa Sojin Nijar wa’adin mayar da Bazoum kan mulki

Shugabannin kasashen kungiyar tattalin arzikin Afirka ta yamma ECOWAS, sun bai wa sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar wa’adin kwana bakwai su mayar da hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum kan mulki.

Wannan dai shi ne matakin da kungiyar ta dauka a taron da ta gudanar ranar Lahadi a Abuja, babban birnin Najeriya.

ECOWAS ta yi kira ga hukumomin sojin na Nijar da su gaggauta sakin shugaba Bazoum, tare da mayar da mulki hannun farar hula a kasar.

A sanarwar da babban jami’inta Omar Touray ta fitar, kungiyar ta ce ta yi watsi da takardar ajiye aiki da aka yi ikirarin cewa daga shugaba Bazoum take.

A yayin da ECOWAS ke Allah wadai da ci gaba da tsare Shugaba Bazoum, ta kuma umurci dukkanin hafsan hafsoshin tsaro na kasashe mambobin kungiyar da su ci gaba da gudanar da wani taron gaggawa don tsara dabarun aiwatar da ayyukan soji na maido da tsarin mulki a kasar.

Daga cikin matakan da kungiyar ta dauka akwai rufe kan iyakokin tudu da na sama tsakanin Nijar da mambobin kungiyar tare da haramta wa jiragen sama da suka taso ko suka nufi Nijar ketawa ta sararin samaniyar kasashen kungiyar ECOWAS.

Haka kuma, ECOWAS ta dakatar da huldar kasuwanci da ta kudi tsakanin Nijar da kasashen kungiyar.