ECOWAS ta sa ranar shiga Nijar da yaƙi

ECOWAS ta ce zaɓi ya rage wa masu juyin mulkin Nijar tsakanin shiga yaƙi ko kuma hawa teburin sulhu

ECOWAS ta sa ranar shiga Nijar da yaƙi

Mahalarta taron Manyan Hafsoshin Tsaron ECOWAS a birnin Accra na Ghana. (Hoto: Reuters/Francis Kokoroko)

Ƙungiyar ECOWAS ta cim-ma matsaya kan lokacin da dakarunta na ko-ta-kwana za su ƙaddamar da hari a jamhuriyar Nijar domin dawo da Shugaba Mohamed Bazoum kan kujerarsa, bayan sojojin da suka yi masa juyin mulki sun yi wa ƙungiyar taurin kai.

Kwamishinan Tsaro da Zaman Lafiya na ECOWAS, Abdel-Fatau Musah, ya ce yanzu zaɓi ya rage wa masu juyin mulkin tsakanin yaki da ECOWAS ko kuma hawa teburin shulhu da kungiyar. Sai dai kuma bai bayyana hakikanin ranar da za a kaddamar da harin ba.

“An cim-ma matsaya kan lokacin shiga Nijar da yaki, kuma mun yi ittifakin kammala tsara abubuwan da muke bukata wajen aiwatar da matakin.

“Muddin dukkanin hanyoyi suka gaza, to jajirtattun dakarun ECOWAS a shirye muke mu je filin-daga,” in ji shi.

Ya ce duk da haka, har yanzu ƙungiyar ta fi son amfani da hanyoyi na diflomasiyya, don haka, za ta “tura wata tawaga ta musamman zuwa Nijar, saboda haka ba mu riga mun toshe kofar tattaunawa da su ba.”

Wannan na zuwa ne bayan taron manyan hafsoshin tsaron ECOWAS, inda suka yanke shawarar ɗaukar matakin soji kan Nijar.

Manyan Hafsoshin Tsaron na ECOWAS sun jaddada dakarunsu na ko-ta-kwana na cikin shirin, abin da suke jira shi ne umarnin tafiya filin-daga.

Taron manyan hafsoshin tsaron na ECOWAS da aka kammala ranar Juma’a a birnin Accra na ƙasar Ghana ya mayar da hankali ne kan daukar matakin soji domin maido da Bazoum kan kujerarsa idan sojojin da suka hamɓarar da shi suka ki amincewa da hawa teburin sulhu.

Taron kwana biyun an gudanar da shi ne bayan sojojin Nijar ƙarƙashin jagorancin Janar Abdoulrahmane Tchiani sun yi watsi da barazana da kuma wa’adin da ƙungiyar ta ba su na dawo da Bazoum kan kujerarsa.

Tun ranar 26 ga wata jiya da sojojin suka kifar da gwamnatin farar hukar suke tsare da Bazoum.

A ranar Juma’a shugaba ECOWAS, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na Najeriya ya yi musu gargaɗi cewa kada su kuskura wani abu ya samu Bazoum.

Kasashe 10 na ECOWAS mai mambobi 15 sun amince su ba da dakaru ga rundunar, in banga guda biyar da suka ki — Cape Verde dak kuma kasashe uku da ke ke karkashin gwamnatin soji, Mali, Burkina Faso da Guinea Bissau).

Sai dai kuma daukar matakin sojin ba zai yiwu kai-tsaye ba, sai bayan cika wasa matakai da suka hada da samun goyon bayan majalisun dokokin kasashen da ke cikin kungiyar.

Yawancin majalisun dokokin kasashen na adawa da daukar matakin soji, ciki har da majalisar dokokin Najeriya da ke jagorantar kungiyar.