ECOWAS ta sake kakaba wa Nijar sabon takunkumi

Sai dai kungiyar ba ta yi cikakken bayani ba a kan matakin

ECOWAS ta sake kakaba wa Nijar sabon takunkumi

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu

Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) ta sake kakaba sabbin takunkumai ga gwamnatin mulkin soja ta Jamhuriyar Nijar.

A baya dai kungiyar ta ba sojojin da suka yi juyin mulki wa’adin kwana bakwai su mayar da hambararren Shugaban Kasar, Mohammed Bazoum, kan karagarsa, ko su mamaye kasar.

Amma sojojin sun yi kunnen uwar shegu da matakin na kungiyar, inda ta ce za ta tsaya kai da fata wajen ganin ta kare kasarta daga kowacce irin barazana daga waje.

Kazalika, Nijar din ta kuma sanar da datse alaka tsakaninta da Najeriya da Togo da Amurka da kuma Faransa, sannan ta rufe sararin samaniyarta har sai abin da hali ya yi.

Sai dai bayan cikar wa’adin, ECOWAS ta kuma kira wani taron na gaggawa da za a yi ranar Alhamis mai zuwa domin duba halin da ake ciki a kasar da kuma daukar mataki na gaba.

Da yake jawabi ga manema labaran Fadar Shugaban Najeriya da ke Abuja, Kakakin Shugaba Bola Tinbu, Ajuri Ngelale, ya ce an kakaba takunkuman ne a kan daidaikun mutane da kungiyoyin da suke kowacce irin hulda da gwamnatin sojan ta Nijar.

Kodayake bai yi cikakken bayani ba, amma ya ce an aiwatar da takunkumin ne ta hannun Babban Bankin Najeriya (CBN).

A kwanakin baya ne dai sojojin na Nijar suka hambarar da gwamnatin Mohammed Bazoum, lamarin da ya jawo daga kungiyoyi da kasashe daban-daban.

Tinubu ya yi naɗin sabbin muƙamai huɗu

Majalisar Zartarwa ta amince da kusan Naira tiriliyan 50 Kasafin Kuɗin 2025

Tinubu ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa

HOTUNA: Ana shirye-shiryen jana’izar marigayi Lagbaja