ECOWAS ta zabi Buhari ya jagoranci yaki da COVID-19
Shugabannin kasashe mambobin Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) sun zabi Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya jagoranci yaki da cutar coronavirus a fadin yankin. Mai bai wa Shugaban Kasa Shawara ta Fuskar Yada Labarai Femi Adeshina ne ya tabbatar wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) da hakan a karshen wani […]
Shugabannin kasashe mambobin Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) sun zabi Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya jagoranci yaki da cutar coronavirus a fadin yankin.
Mai bai wa Shugaban Kasa Shawara ta Fuskar Yada Labarai Femi Adeshina ne ya tabbatar wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) da hakan a karshen wani taron gaggawa da shugabannin suka gudanar.
NAN ya ruwaito cewa taron, wanda shugabannin suka kirawo, ya mayar da hankali ne kacokan a kan annobar COVID-19 wacce take ci gaba da daukar rayukan jama’a a fadin duniya.
Da yake bude taron, shugaban ECOWAS, wanda kuma shi ne shugaban kasar Jamhuriyar Nijar, Muhammadu Issoufou, ya ja hankalin sauran takwarorin aikinsa a kan irin illar da wannan annoba take yi a kan bil-Adama da kuma tattatin arzikin kasashen da ke wannan kungiya.
Haka kuma Mahamadou Issoufou ya jinjina wa Bankin Duniya da kuma Bankin Raya Kasashen Afirka (AfDB) a kan irin rawar da suke takawa wajen dakile yaduwar cutar a nahiyar Afirka, sannan ya nemi su ci gaba da ba da gudunmawa don ceton rayukan al’umma.
Kimanin shugabannin kasa 13 ne ciki har da Shugaba Buhari suka halarci wannan taro.