ECOWAS za ta yi sabon taro kan juyin mulkin soji a Nijar
ECOWAS za ta yi taron ne don sanin matakin da za ta dauka a kan Nijar.
Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasasahen Yammacin Afirka (ECOWAS), za ta gudanar da taron koli a Abuja don tattauna batun Nijar, bayan cikar wa’adin da ta bai wa sojojin da suka yi juyin mulki a kasar.
Aminiya ta ruwaito Jamhuriyar Nijar ta rufe sararin samaniyarta bisa fargabar yiwuwar kai mata farmaki, bayan da sojojin da suka yi juyin mulki a kasar suka yi kunnen uwar shegu da wa’adin da ECOWAS ta gindaya.
asancewar kungiyar ta yi barzanar afka wa kasar da yaki matukar sojoji suka yi kunnen kashi
- Wa’adin ECOWAS: Sojojin Nijar sun yi shirin ko-ta-kwana
- Makarantu 79 na da malami 1 kowannensu a Bauchi
Burkina Faso da Mali sun ce za su tura tawagar hadin gwiwa domin nuna goyon baya ga Nijar.
Sai dai gwamnatin mulkin soji a Jamhuriyar Nijar ta rufe sararin samaniyarta bisa fargabar yiwuwar kai mata farmaki.
Mambobin ECOWAS sun samu rabuwar kai kan daukar matakin sojin, wanda shugaban kungiyar kuma na Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bukata.
Sai dai a wani yunkuri na kare kai daga shirin ECOWAS, shugaban dakarun sojin da ya jagoranci hambarar da gwamnatin shugaba Mohamed Bazoum, Janar Abdourahamane Tchiani, ya nemi hadin kan kasar Rasha.
Shi ma a nasa bangaren, shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya gana da gwamnonin Katsina, Kebbi da Jigawa a Fadar Gwamnatin Najeriya a wani yunkuri na daukar mataki a kan Nijar.
Tuni dai shugabannin kasashen duniya da dama suka yi Allah-wadai da juyin mulki da sojojin fadar shugaban kasar Nijar suka yi.
Kazalika, juyin mulki ya sanya kasashe da dama ciki har da Amurka da Faransa janye tallafi da suke bai wa Nijar.