Ecuador ta lallasa Qatar a wasan farko na Gasar Kofin Duniya
Valencia ya kara kwallo da ci 2-0 kafin a tafi hutun rabin lokaci.
Kasar Qatar da ke yi wa Gasar Kofin Duniya masaukin baki ta fara da kafar hagu yayin da ta kwashi kashinta a hannu a wasan farko da ta fafata da Ecuador.
Wannan ne karo na farko da mai masaukin baki ta yi rashin nasara, tun daga farkon fara gasar a shekarar 1930.
- Sauyin Yanayi: Manyan kasashe za su tallafawa matalauta
- Mu’ammar Gaddafi: Shekara 11 da kisan Shugaban Libya
A 1930 dai mai masaukin baki Uraguay, ta kai har wasan karshe kuma ta yi nasarar lashe kofin, bayan ta ta yi wa Ajentina luguden ci 4:2.
A ranar Lahadi ne aka fara Gasar Kofin Duniya a kasar Qatar, a daidai lokacin da aka fara gudanar da wasan kwallon kafa na tsawon wata guda, bayan da aka shafe shekaru 12 ana tafka muhawara kan karbar bakuncin gasar.
Sheikh Tamim bin Hamad Al-Thani, Sarkin Qatar ya halarci babban filin wasa na Al Bayt da ke Al Khor mai tazarar kilomita 50 a wajen Doha, domin kallon wasan da kasar ta kara da Ecuador.
A wasan da aka fara ba kakkautawa a filin wasa mai kama da tanti na Bedouin, Enner Valenica na Ecuador ya zura kwallon a raga bayan mintuna uku amma alkalin wasan ya soke kwallon sakamakon satar gida.
Bayan mintuna 13 ne Ecuador ta kuma zura kwallon bayan da Valencia ya zurawa mai tsaron ragar Qatar Saad Alsheeb a bugun daga kai sai mai tsaron gida.
Valencia ya kara kwallo da ci 2-0 kafin a tafi hutun rabin lokaci.
Filin wasan na Al Bayt na daya daga cikin jerin sabbin filayen wasa da aka gina domin gudanar da gasar, wanda aka kiyasta cewa Qatar ta kashe dala biliyan 200, wanda ya zama gasar cin kofin duniya mafi tsada a tarihi.
Tauraron K-pop na Koriya ta Kudu Jung Kook ya jagoranci bikin bude taron na mintuna 30 wanda tauraron Hollywood Morgan Freeman ya kasance shugaban taron.
Ghanim Al-Muftah, dan gwagwarmaya ga nakasassu a kasar Qatar, tare da Freeman sun yi wa mahalarta taron “maraba”.