Edita ta kasa dauko labarin danta da ya yi harbin kan-mai-uwa-da-wabi
Editar jaridar the Marshall County Daily da ke garin Benton a Jihar Kentucky a Amurka ta yi hanzari zuwa wata babbar makarantar sakadanre da dalibi ya yi harbe-harbe don dauko labari da dumi-duminsa, amma sai ta karke da gano cewa danta ne wanda ake tuhuma da harbin. Ta ziyarci makarantar ba wai don kawai ta […]
Editar jaridar the Marshall County Daily da ke garin Benton a Jihar Kentucky a Amurka ta yi hanzari zuwa wata babbar makarantar sakadanre da dalibi ya yi harbe-harbe don dauko labari da dumi-duminsa, amma sai ta karke da gano cewa danta ne wanda ake tuhuma da harbin.
Ta ziyarci makarantar ba wai don kawai ta kawo rahoton al’amarin da ya auku ba, saidondanta ma dalibi ne a makarantar ta Marshall County High. Da isarta wajen, sai ta gano babban abin tashin hankali. Domin danta ne hakikanin wanda ake zargi da akata harbe-harben.
A cewar jami’an tsaro, GabeParker dan shekara 15 ya shiga makaranta da sanyin safiya, inda ya bude wa dalibai wuta da karamar binddigar hannu, har ya kashe mutum biyu ya raunata wasu mutum 14 kafin an ankara cewa shi ne ya aikata lafin. Biyar daga cikin wadand aaka harba suna cikin halin rai kwakwai,mutum kwakwai.
Wasu daliban sun samu raunuka ne a lokacin da suka yi kokarin tsira daga halaka, yayin da wasu suka yi mil guda a kan titin don su samu tsira.
Mahaifiyar Parker,Mary Garrison Minyard ba ta bayar da wata sanarwa a bainar jama’a ba, domin a zahiri mahar shafinta na facebook ta goge bayan da aka yi harbe-harben.
Harbin kan mai uwa da wabi da aka yi a makarantar Marshall High shi ne irin sa na farko a wannan shekarar ta 2018. Har yanzu dai ba a gano manufar Parker ta yin wannan harbin ba, amma mai gabatar da kara na yankin, Mark Blankenship ya bayyana wa Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters a sakon i-mail cewa wanda ya yi harbi ya yi ne kan mai uwa da wabi.
Gwamnan Kentucky, Matt Bebin a taron ’yan jarida ya bayyana cewa za a tuhumi Parker da kisan kai da kuma yunkurin yin kisa. “Wannan rauni ne da zai dade bai warke ba, kuma wasu ma ba za su warke da kyau ba,” inji Bebin.
Hukumomi na databbacin cewa Parker ya yi aiki ne a kashinkansa shi kadai. “babu alamun da suka nuna akwai wani mutum da ya hada kai da shi a wani wuri,” a cewar Kwamishin ‘’yan sandan Kentucky, Rick Sanders a taron ’yan jarida.
Sai dai wani abokin harkokin siyasarsa. Stebe Westa, dan jam’iyyar Republican kuma dan majalisar dattijai da ke wkailtar jihar, ya gabatar da doka a wannan makon da za ta bai w amakarantu damar daukar kwararrun masu sarrafa bindiga don ssu bai wa dalibai kariya
Bebin, dan jam’iyyar Repiublican, kuma mai ra’ayin rikau ya ce ba zai matsakan cewa a tabbatar da dokar takaita amfani da bindiga ba,bayan aukuwar lamarin, inda ya kira harbe-harben makaranta a matsayin “mummunar al’ada” a wajen wani taro da aka gudanar ranar Juma’a.
Sauran ’yan majalisar wakilai da suka fito daga jam’iyyar Democrat daga jihar, wato irin su Attica scot mai wkailtar Louisibille ta ce , “tabbas ita mai fafutikar ganinan bayar da kariyar bindiga ce, don haka take kokarin ganin an tsarurara doka ga masu sayar da bindiga.”