Editan shafin sadarwar Saudiyya zai yi kurkukun shekara bakwai da bulala 600
An yanke wa Editan Shafin sadarwar masu ra’ayin ’yanci a Saudiyya daurin shekara bakwai da bulala 600. Raif Badawi, wanda ya kirkiro da shafin “Free Saudi Liberals” inda suke tattaunawa kan matysayin addinmi a Saudiyya, yana tsare tun cikin watan Yunin 2012, inda ake tuhumarsa da aikata laifin yada barnar ta hanyar shafukan intanet, tare […]
An yanke wa Editan Shafin sadarwar masu ra’ayin ’yanci a Saudiyya daurin shekara bakwai da bulala 600. Raif Badawi, wanda ya kirkiro da shafin “Free Saudi Liberals” inda suke tattaunawa kan matysayin addinmi a Saudiyya, yana tsare tun cikin watan Yunin 2012, inda ake tuhumarsa da aikata laifin yada barnar ta hanyar shafukan intanet, tare da saba wa mahaifinsa.
Editan ya nuna ba ruwansa da addini, a halin yanzu yana da ’ya’ya biyu mata da da daya.
Jaridar Al-Watan ta ruwaito cewa, alkalin da ya yanke wa Editan hukunci, ya kuma bayar da umarnin a rufe shafin.
Ma’aikatar Harkokin wajen Faransa, ta yi matukar nuna damuwarta kan lallai a jajirce “wajen bayar da ’yancin fadin albarkacin baki da bayyana ra’ayi.”
Masu fafutikar ganin an saki wannan edita, sun yada cewa shari’a na yaduwa daga Saudiyya zuwa Iran da Iraki da Aljeriya, ga Masar ta kunno kai a kusa da ku. Idan aka yi wasa za a wayi gari da ita a babban birnin Faransa Paris ko birnin Landan ya zama Londonistan ko Copenhagen ta zama Shariahagen. Azaba! Mun gode kwarai!! A saki Raif Badawi yanzu!