EFCC ba ta da hurumin gurfanar da alkalai-Kotu
Kotun daukaka kara jiya ta zartar da hukuncin cewa Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da Ta’annutin Kudi ta EFCC ba ta da hurumin bincike tare da gurfanar da alkalai da suke kan aiki. Kotun wacce Mai shari’a Adejumo Obaseki yake yi wa alkalanci a Legas ta bayyana cewa hukumar za ta iya gurfanar […]
Kotun daukaka kara jiya ta zartar da hukuncin cewa Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da Ta’annutin Kudi ta EFCC ba ta da hurumin bincike tare da gurfanar da alkalai da suke kan aiki.
Kotun wacce Mai shari’a Adejumo Obaseki yake yi wa alkalanci a Legas ta bayyana cewa hukumar za ta iya gurfanar da alkalan ne kawai bayan cibiyar shari’a ta kasa ta kore su daga aiki.