EFCC na neman matar Emefiele ruwa a jallo

EFCC na neman Margaret Emefiele da Eric Odoh, da Anita Omolie da kuma Jonathan Omolie.

EFCC na neman matar Emefiele ruwa a jallo

Hukumar Hana Yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati EFCC ta ayyana neman uwar gidan tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele ruwa a jallo.

Hukumar na neman Margaret Emefiele, da wasu karin manyan kusoshin bankin a zamanin sa da suka hadar da Eric Odoh, da kuma wata fitaciyyar ‘yar kasuwa Anita Omolie da kuma wani rikakken dan canji Jonathan Omolie.

Cikin wata sanarwa da Dele Oyewale, jami’in hulɗa da al’umma na EFCC ya fitar ya ce ana zargin mutanen ne da haɗa baki da shi Emefiele wajen karkatar da wasu makudan kuɗaɗe mallakin Gwamnatin Tarayya lokacin da yake jagorantar bankin.

Bayanai sun ce, uwargidan tsohon gwamnan na CBN ta buya a wani waje da ba a sani ba a Najeriya, tun bayan da aka kama mai gidanta.

Hukumar ta kuma wallafa hotunan mutanen da take neman din a shafinta na sada zumunta tare da rokon jama’a da su sanar da ita da zarar an gansu.

Wallafar ayyana nema ruwa a jallo da EFCC ta yi kan mutanen huɗu.

Wannan dai na zaman wata karin hujja ga hukumar, a ci gaba da shari’ar da ake tafkawa tsakanin ta da Emefiele, wanda aka kama tun a ranar da shugaba Tinubu ya sanar da sauke shi daga mukamin sa.

Ana zargin Emefile da cin hanci da rashawa, karkatar da kudaden kasa da halasta kudaden haramun, da kuma sanya son zuciya da sanayya a aikin sa, lamarin da ya jefa miliyoyin ‘yan Najeriya cikin tashin hankali.

Emefiele, wanda aka gurfanar da shi a ranar 18 ga watan Nuwamba, 2023, ya ki amsa tuhumar da ake masa na tuhume-tuhume shidan farko.

A ranar 22 ga watan Nuwamba wata Babbar Kotun Tarayya ta bayar da belinsa a kan kuɗi naira miliyan 300.

A zaman da ya gabata, kotun ta amince da sauya sharaɗin belin Emefiele wanda a baya aka takaita masa talala iya babban birnin tarayya Abuja kaɗai.

Kotun ta amince da buƙatar da ta bai wa tsohon gwamnan CBN izinin tafiye-tafute a cikin Najeriya amma ta hana shi fita daga kasar a yayin da ake ci gaba da shari’ar.

Mai hannu ɗaya da ke sana’ar faskare

Dole talauci ya yi katutu a Arewa!

Hauhawar farashin kayayyaki ta ƙaru da kaso 33 a Najeriya — NBS

Kotun Ƙoli ta yi watsi da buƙatar rushe Hukumar EFCC