EFCC sun rufe shagunan motoci da kwace motoci 29

Reshen ofishin Hukumar EFCC da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta’annati da ke jihar Legas sun kwace motocin alfarma 29 a wani samame da Hukumar ta kai ofishin dilar motocin na Astrax Auto Shop. Hukumar ta kai samamen ne bayan wani rahoto da suka samu akan yadda shagunan motocin ke gudanar […]

EFCC sun rufe shagunan motoci da kwace motoci 29

Reshen ofishin Hukumar EFCC da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta’annati da ke jihar Legas sun kwace motocin alfarma 29 a wani samame da Hukumar ta kai ofishin dilar motocin na Astrax Auto Shop.

Hukumar ta kai samamen ne bayan wani rahoto da suka samu akan yadda shagunan motocin ke gudanar da harkokin kasuwacinsu wanda suke tuhumarsu nada alaka da damfara ta hanyar intanet.

Motocin da Hukumar EFCC ta kwace sun hada da: Toyota Corolla (4); Toyota Camry (7); Toyota Highlander (2); Toyota Venza (2); Range Rover (2); Ford SUV (1); Mercedes Benz (3); Toyota 4runner (1); Toyota Sienna (1); Honda Accord (4); Toyota Sequoia (1) da kuma Kia (1).