EFCC ta bankaɗo sabuwar badaƙalar fiye da N100bn kan Yahaya Bello
Lamarin dai na zuwa ne daidai lokacin da tsohon gwamnan ya ke ’yar wasan ɓuya da mahukunta EFCC.
Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), ta gabatar wa wata Babbar Kotu a Abuja sabbin tuhume-tuhume 16 da suka shafi zamba da take zargin tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello ya aikata.
Tuhume-tuhumen da Gwamnatin Tarayya ta shigar ta hannun lauyoyin EFCC, Kemi Pinheiro da Rotimi Oyedepo da wasu lauyoyi 7, sun ƙara haɗa Umar Shuaibu Oricha da Abdulsalam Hudu a matsayin waɗanda ake zargi tare da Yahaya Bello.
- HOTUNA: Yadda ambaliya ta mamaye yankuna 82 da makarantu 90 a Neja
- Kotu ta kori bukatar APC na hana zaben kananan hukumomin Kano
Lamarin dai na zuwa ne daidai lokacin da tsohon gwamnan ya ke ’yar wasan ɓuya da mahukunta EFCC da kuma ƙin halartar wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja da suke tuhumarsa kan sace zunzurutun kuɗi har Naira biliyan 80.2 a lokacin da yake riƙe da madafun iko a jihar.
A ƙunshin sabbin tuhume-tuhumen, EFCC ta bayyana cewa ta bankaɗo wani sabon zamba da ake zargin tsohon gwamnan da ya kai har N110,446,470,089.00.