EFCC ta cafke Kakakin Majalisar Ogun a filin jirgin saman Legas

Ana dai zarginsa ne da karkatar da kudaden majalisar

EFCC ta cafke Kakakin Majalisar Ogun a filin jirgin saman Legas

Kakakin Majalisar Ogun, Olakunle OLuomo

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC ta cafke Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Ogun, Olakunle Oluomo.

EFCC ta kama shi ne da sanyin safiyar Alhamis a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Legas.

An dai kama shi ne bisa zargin badakalar wasu kudade, bayan jami’an hukumar sun sami bayanan sirri a kan yunkurin tafiyarsa.

Wata majiya ta shaida mana cewa yanzu haka Kakakin na can yana fuskantar titsiye a hannun jami’an hukumar.

Majiyar, wacce ta nemi a sakaya sunanta ta kuma ce dama sunansa ya jima a jerin sunayen wadanda hukumar ke nema ruwa a jallo bayan ya ki amsa gayyatar da ta yi masa a baya.

An dai zarginsa tare da wasu mutane da satar sa-hannu domin karkatar da kudaden majalisar.

Sai dai da wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin Kakakin EFCC a ofishinta na shiyya da ke Legas, Ayo Oyewole, hakarsa ta gaza cim ma ruwa,  saboda ya ki amsa kiran wayarsa.