EFCC ta cafke kanin Hadi Sirika kan badakalar N8bn

Hukumar EFCC tsare kanin tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika kan badakalar N8b a lokacin da wansa ke minista

EFCC ta cafke kanin Hadi Sirika kan badakalar N8bn

Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika

Hukumar yaki da masu karya tattalin arzikin kasa (EFCC) ta kama Abubakar Ahmad Sirika, kanin tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika.

EFCC ta kama Ahmad Sirika ne a ranar Lahadi, kan binciken da hukumar ke yi a kan ma’aikatar sufurin jiragen sama badakalar Naira biliyan 8 a karkashin Hadi Sirika.

Ana zargin a lokacin shugabancin Hadi ne aka ba Ahmad kwangila, duk da kasancewar ma’aikacin gwamnati a mataimakin darakta a mataki na 16.

A lokacin shugabancin Hadi Sirika an zarge shi da hada baki, badakala, karkatar da kudaden jama’a, kara farashin kwangila, da kuma karkatar da kudaden da suka kai N8,069,176,864.

EFCC ta bayyana cewa kudin da ake bincike a kansu, na kwangilar jiragen sama guda hudu ne da tsohon ministan ya ba wa kamfani mallakin kanin nasa mai suna Engirios Nigeria Limited.

Hukumar ta kara da shugaban kamfanin, Abubakar shi kadai ne ke sanya hannu kan asusun ajiyar kamfanin guda biyu.

An ceto jaririyar da ’yar aikin gida ta sace a Edo

An ceto mutum 58 da aka sace a Kaduna

Sarkin Zazzau ya naɗa sabbin hakimai 7

Hajjin 2025: Maniyyata za su fara ajiye N8.4m a Kaduna