EFCC ta cafke Obi Cubana

Ana zarginsa kan batun halatta kudin haram da kin biyan haraji.

EFCC ta cafke Obi Cubana

Obi Cubana

Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati a Najeriya, ta cafke fitaccen mai wadaka da dukiya, Obinna Iyiegbu, da aka fi sani da Obi Cubana, kan zargin halatta kudin haram.

Kafofin Yada Labarai a Najeriya sun ruwaito cewa, a ranar Litinin ne Obi haifaffen Jihar Anambra ya isa Babban Ofishin Hukumar EFCC da ke Unguwar Jabi a Abuja, babban birnin kasar, domin ya amsa tambayoyi kan zargin da ake masa.

Duk da cewa zarge-zargen da ake yi wa Obi ba su da yawa, amma wata majiya ta ce batun halatta kudin haram da kin biyan haraji na daga cikin abubuwan da ake tuhumarsa a kai.

Majiyar ta kara da cewa, “An kama Obi Cubana ne a ranar Litinin da rana, aka kuma tasa keyarsa zuwa Babban Ofishin hukumar EFCC, kan wadancan zarge-zarge da na bayyana.

“A yanzu haka yana can masu tuhuma suna titsiye shi da tambayoyi.”

Sai dai da aka tuntubi Mai Magana da Yawun Hukumar EFCC, Wilson Uwujaren, bai ce uffan kan batun ba.

A watan Yuli ne sunan Obi Cubana ya yi tambari a ciki da wajen Najeriya, lokacin da ya yi gagrumin bikin binne mahaifiyarsa da ta rasu a birnin Oba da ke jihar Anambra inda aka yanka shanu 200 a wannan lokacin.

Haka kuma yadda aka dinga holen dukiyarsa da yadda ya ke facaka da kudi, ya janyo sanya ayar tambaya a zukatan ’yan Najeriya kan hanyar da ya ke samun kudi.

Fitattun mutane da ’yan siyasa daga sassa daban-daban na Najeriya ne suka yi tururuwa a bikin binne mahaifiyar Obi a watan Yulin shekarar nan.