EFCC ta fara bincike kan Dala biliyan 16 da aka kashe kan samar da lantarki

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ta fara binciken kudin da ake zargi sun bace kan aikin wutar lantarki a gwamnatin tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo. Hukumar za ta soma kama wadansu da ake zargi da sace tiriliyoyin Naira bayan gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta ce za a binciki badakalar da aka […]

EFCC ta fara bincike kan Dala biliyan 16 da aka kashe kan samar da lantarki

Tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ta fara binciken kudin da ake zargi sun bace kan aikin wutar lantarki a gwamnatin tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo. Hukumar za ta soma kama wadansu da ake zargi da sace tiriliyoyin Naira bayan gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta ce za a binciki badakalar da aka tafka a baya. A dalilin wannan bincike tuni jami’an Hukumar EFCC suka kama wadansu ma’aikatan Kamfanin Lantaki na Neja Delta (NDPHC).

Sai dai Tsohon Shugaban Kasa Obasanjo yana ikirarin cewa bai yi awon gaba da ko kwabo da aka ware don samar da lantarkin ba. Ana zargin gwamnatin Olusegun Obasanjo da batar da Dala biliyan 16 wajen samar da wutar lantarki inda kawo yau ake kukan rashin isasshiyar wutar lantarki a kasar nan bayan kashe makudan kudaden.

Hujjar da Obasanjo ke bayarwa ita ce an kashe wadannan kudi ne wajen ayyukan da Hukumar NNIPP ta yi da gina na’urorin samar da wuta na gas 18 shekara fiye da goma da suka wuce. EFCC ta sha alwashin zakulo duk wanda yake da hannu wajen karkatar da kudin wutar. Tuni dai aka fara bincikar jami’an Hukumar NDPHC kan zargin wawure sama da Naira biliyan 80. Aminiya ta gan ana tunanin cikin ’yan kwanakin nan za a sake kama wadansu jami’an  da ake zargi da hannu a badakalar da aka tafka a lokacin mulkin PDP.

Daga cikin wadanda za a yi wa tambayoyi a ’yan kwanakin nan akwai wani tsohon Shugaban Hukumar TCN wanda ya karbi Naira biliyan 185 domin shigo da wasu manyan na’urorin samar da wutar lantarki.