EFCC ta fara binciken gidajen Shehu Sani a Abuja
Jami’an Hukumar Yaki da Yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) na bincken wasu gidaje biyu a Abuja mallakar tsohon Sanata mai Wakiltar Kaduna ta tsakiya Shehu Sani. Rahoton na bayyana cewa jami’an EFCC sun samu izinin binciken gidajen daga Kotun Majistare da ke Abuja a wani bangare da na tuhumar da kotun ke yi wa […]
Shehu Sani
Jami’an Hukumar Yaki da Yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) na bincken wasu gidaje biyu a Abuja mallakar tsohon Sanata mai Wakiltar Kaduna ta tsakiya Shehu Sani.
Rahoton na bayyana cewa jami’an EFCC sun samu izinin binciken gidajen daga Kotun Majistare da ke Abuja a wani bangare da na tuhumar da kotun ke yi wa Shehu Sani.
Hukumar ta EFCC ta tsare Shehu Sani, akan tuhumarsa na wasu kudade da suka kai dalar Amurka dubu $24 daidai da Naira miliyan 8 da dubu dari 7 da dubu 4 da dari 350 da kuma 22 (N8704350.22) daga wurin shugaban Kamfanin motocin ASD Motors, Sani Dauda.