EFCC ta fara binciken shugaban hukumar yaki da cin hanci ta Kano

Ana binciken ne a daidai lokacin da Muhuyi ke binciken Ga duke kan bidiyon Dala

EFCC ta fara binciken shugaban hukumar yaki da cin hanci ta Kano

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) da Hukumar Kula da Da’ar Ma’aikata (CCB) sun fara binciken shugaban Hukumar Karbar Koke-koke da Yaki da Rashawa ta Jihar Kano, Muhuyi Magaji Rimin Gado.

A cikin wata wasika da Mataimakin Darakta a EFCC, Mukhtar S. Bello, ya fitar hukumar ta gayyaci Daraktan Kudi na hukumar da Muhuyi yake wa jagoranci da ya bayyana a hedkwatarta da ke Abuja ranar Litinin.

A cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan 8 ga watan Agusta, wacce Aminiya ta gani ranar Lahadi ta bukaci Daraktan ya je hukumar da rahoton kudaden da suka kashe a shekara ta 2021.

Wasikar ta kuma ce, “Muna bukatar ka zo da rahoton kudaden da Ma’aikatar Kananan Ya Jihar Kano ta tura mata daga 2019 zuwa 2021, ciki har da kwangilolin da aka bayar da kuma mutanen da aka ba.”

A nata bangaren, hukumar CCB, a cikin wasika mai dauke da kwanan watan 14 ga watan Agusta, ta ce tana bincike ne a kan zargin karya dokar da’ar ma’aikata a hukumar.

“A kan haka ne aka bukaci Muhuyi ya gabatar da takardun ainihi da ke dauke da cikakkun bayanan dukkan ma’aikata na abin da ya shiga da wanda ya fita da kwangilolin da aka yi da dukkan kudaden da ta kashe tun daga 2016 har zuwa yau,” in ji CCB.

Aminiya ta gano cewa binciken na zuwa ne a daidai lokacin da hukumar Muhuyi ta fara bincike a kan bidiyon Dala na tsohon Gwamnan Kano, kuma shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje.

Sai dai Ganduje ya samo wani kwarya-kwaryar hukuncin kotu da ya hana hukumar bincikensa tare da iyalansa da makusantansa, amma hukumar ta kama tsohon Shugaban Kamfanin KASCO ma Jihar, Bala Inuwa, kan zargin badakalar Naira biliyan 4.3.

Amma da Aminiya ta tuntube shi, Muhuyi Magaji ya ce za su hada gwiwa da sauran hukumomin domin ba su dukkan bayanan da suke nema daga wajen su.

Tsofaffin ma’aikatan Gombe 2,204 sun karɓi giratuti N4.2bn

Bam ya yi ajalin ɗaliban Islamiyya 2 a Abuja 

Mamakon ruwan sama ya haddasa ambaliya a Saudiyya

’Yan sanda sun ceto yara 4 da aka sace daga Bauchi a Anambra