EFCC ta gabatar da wanda ake zargi da damfarar Naira miliyan 10 a Kotu

Hukumar Yaki da yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati shiyyar Kudu maso Gabas (EFCC), inda ta gabatar da Justus Russell Manajan Reshen Cibiyar Hada-Hadar kudi da zuba Jari mai suna BestworthAssets and Trustlimited da ke birni Benin a Jihar Edo gaban kotu mai daraja ta biyu, bisa zarginsa da aikata zamba cikin aminci ta kudi […]

EFCC ta gabatar da wanda ake zargi da damfarar Naira miliyan 10 a Kotu
EFCC ta gabatar da wanda ake zargi da damfarar Naira miliyan 10 a Kotu

Hukumar Yaki da yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati shiyyar Kudu maso Gabas (EFCC), inda ta gabatar da Justus Russell Manajan Reshen Cibiyar Hada-Hadar kudi da zuba Jari mai suna BestworthAssets and Trustlimited da ke birni Benin a Jihar Edo gaban kotu mai daraja ta biyu, bisa zarginsa da aikata zamba cikin aminci ta kudi Naira milyan 10.

Mista Russell ya gurfana gaban alkalin kotu ta biyu Mai shari’a C.F. Ikponmwen bisa tuhumarsa da laifuka hudu da ake zargi ya aikta, kuma ake bukatar ya yi wa kotun bayani kan badakalar kudin da yin amfani da sunan bogi ya yi damfara .
Yadda asirin manajan ya tonu kuwa kamar yadda Aminiya ta samu labara, wani dan kasuwa mazaunin birnin Benin mai suna Farfesa Austin Obasohan mai Cibiyar kula da lafiyar jama’a mai zaman kanta ta Bupa Medical centre ne ya kai karrarsa gaban kuliya. Sun hada hakar kasuwanci ne, inda ya zuba jari a kamfaninsa lokacin da aka yi ajalin karbar kudi ya cika sai shi wanda ake zargi ya ce ma Farfesa Obasohan cewa “ya daga masa nan da wata uku zai samu kudinsa kamfaninsa na fuskantar wasu ’yan matsaloli kafin wa’adin ya cika za su warware matsalar da kamfanin ya shiga”
Ashe shi Farfesa bai san ma cewa tun shekara ta 2011 ba ne aka kori Imona Russells daga aiki a wannan kamfani, ba tare da nunawa ko sanar wa Farfesa cewa ba ya aiki ba, ya neme shi da su hada huldar kasuwancin zuba jari a kamfaninsa cikin shekara ta 2012. Kuma wanda ake zargi ya ci gaba da karade jama’a yana neman harka da sunan kamfanin da ya koreshi daga aiki Mai gabatar da kara ya tabbatar wa kotu cewa, mai laifin na ci gaba da hulda da jama’a da sunan wannan kamfani da ya kore shi aiki.