EFCC ta gano kadarorin Naira miliyan 500 na Jonah Jang

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta’annati, EFCC ta ce, ta gano kadarorin da suka kai Naira miliyan 500 mallakin tsohon Gwamnan jihar Filato Jonah Jang. Kadarar da aka gano a titin Gobarau mai lamba 8 da 9 Unguwan Rimi GRA jihar Kaduna, kamar yadda  mukaddashshin kakakin hukumar EFCC Tony […]

EFCC ta gano kadarorin Naira miliyan 500 na Jonah Jang

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta’annati, EFCC ta ce, ta gano kadarorin da suka kai Naira miliyan 500 mallakin tsohon Gwamnan jihar Filato Jonah Jang.

Kadarar da aka gano a titin Gobarau mai lamba 8 da 9 Unguwan Rimi GRA jihar Kaduna, kamar yadda  mukaddashshin kakakin hukumar EFCC Tony Orilade ya sanar.

EFCC dai na tuhumar tsohon Gwamnan ne tun a ranar 7 ga watan Mayu 20198 akan wasu laifuka 12 tare da karkatar da kudaden da suka kai Naira biliyan 6.3.