EFCC ta gayyaci shugaban NAHCON kan aikin Hajjin 2024
EFCC ta gayyaci Arabi don bincikar yadda NAHCON ta kashe Naira biliyan 90 a Hajjin bana.
Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arziƙi Zagon Ƙasa (EFCC), ta gayyaci Shugaban Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON), Malam Jalal Arabi, kan yadda hukumar ta kashe Naira biliyan 90 a Hajjin 2024.
EFCC ta sanya ƙarfe 10:00 na safiyar yau a matsayin lokacin da za ta gana da shugaban na NAHCON.
- Dambaruwar NIN: MTN ya kulle dukkanin ofishinsa a Najeriya
- Rushe Masarautun Kano: Ba a kyauta mana ba —Kabiru Rurum
Majiyoyi daga EFCC sun bayyana cewa Arabi zai yi cikakken bayani kan yadda NAHCON ta raba dubban daloli ga alhazai.
Wannan gayyata na daga cikin bincike kan ƙorafe-ƙorafe da dama da aka yi wa NAHCON, ciki har da zargin nuna rashin adalci ga alhazai a Saudiyya yayin aikin Hajjin 2024.
Kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya ce zai tabbatar da cikakken bayanin gayyatar Arabi.
Arabi ya bayyana a baya cewa gwamnati ta tallafa wa kowane Alhaji da Naira miliyan 1.6 saboda karyewar darajar Naira, sakamakon sauye-sauyen musayar kuɗi da Babban Bankin Najeriya (CBN), ya yi.
Arabi, ya kuma ce Gwamnatin Tarayya ta amince tare da biyan Naira biliyan 90 a matsayin tallafi ga Alhazan Najeriya.
Idan ba a manta ba, Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya yi kira da a soke NAHCON saboda rashin jin daɗinsa kan yadda hukumar ta gudanar da aikin Hajjin 2024.
Bago, ya ce hukumar ta gaza samar wa da alhazai magunguna, mazauni da abincin da ya dace duba da irin maƙudan kuɗaɗen da suka kashe domin zuwa aikin Hajji.
Gwamnan ya yi kira ga sauran gwamnonin jihohi su mara masa baya domin rushe hukumar da kuma mayar da al’amuran aikin Hajji hannun gwamnatocin jihohi.