EFCC ta gayyaci tsohon gwamnan Kogi kan miliyan 500

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Ta’annutin Kudi ta EFCC ta yi wa tsohon gwamnan jihar Kogi, Idris Wada tambayoyi kan Naira miliyan 500 kudin kamfe na jam’iyyar PDP. Aminiya ta gano cewa Wada ya isa ofishin EFCC da tsakar rana kuma ana ci gaba yi masa tambayoyi har zuwa lokacin hada wannan rahoto. Hukumra […]

EFCC ta gayyaci tsohon gwamnan Kogi kan miliyan 500

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Ta’annutin Kudi ta EFCC ta yi wa tsohon gwamnan jihar Kogi, Idris Wada tambayoyi kan Naira miliyan 500 kudin kamfe na jam’iyyar PDP.
Aminiya ta gano cewa Wada ya isa ofishin EFCC da tsakar rana kuma ana ci gaba yi masa tambayoyi har zuwa lokacin hada wannan rahoto.
Hukumra EFCC din ta gayyaci tsohon gwamnan don ya yi bayani kan Naira miliyan 500 na kudin zabe da ake zargin ya karba daga wurin tsohuwar Ministar Man Fetur, Diezani Alison-Madueke.