EFCC ta gayyaci tsohon shugaban NIA da sauransu

Hukumar EFCC ta gayyaci tsohon Darakta-Janar na Hukumar Leken Asari ta kasa (NIA), Ayodele Oke domin yi masa tambayoyi a kan Dala miliyan 43,450 da aka gano a Osorborne Towers, Ikoyi Legas. Majiyar Aminiya daga manyan jami’an hukumar ta EFCC ta bayyana cewa gayyatar an yi ta ne saboda ci gaba da bincike domin warware […]

EFCC ta gayyaci tsohon shugaban NIA da sauransu

Hukumar EFCC ta gayyaci tsohon Darakta-Janar na Hukumar Leken Asari ta kasa (NIA), Ayodele Oke domin yi masa tambayoyi a kan Dala miliyan 43,450 da aka gano a Osorborne Towers, Ikoyi Legas.

Majiyar Aminiya daga manyan jami’an hukumar ta EFCC ta bayyana cewa gayyatar an yi ta ne saboda ci gaba da bincike domin warware al’amuran da ke baibaye da wadannan kudin da masu binciken hukumar suka gano a wannan gida, wanda aka ce na hukumar NIA ne.

Haka kuma an samu bayanin cewa an sake gayyatar Oke da matarsa Folashade domin yi musu tambayoyi.

Majiyar t ace uwargidan Oke ta kaurace wa gayyatar ta da EFCC ta yi ta yi mata a baya. hukumar ta ci gaba da binciken al’amarin ne bayan Gwamnatin Tarayya ta yanke hukuncin korar Oke daga kujerarsa ta Darakta-Janar. “Baya ga su biyu, wasu wadanda ake zargi ma an gayyace su domin tantance ko akwai hannunsu a cikin badakalar makudan kudaden da aka gano a gidan na kan titin Osborne, Ikoyi-Legas, da suka hada da na waje da kuma na Najeriya.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kori Ambasada Oke daga mukaminsa na Darakta-Janar a ranar Litinin 30, Oktoba na bana, inda kafin nan, a Afrilun bana, aka dakatar da shi, bayan hukumar EFCC ta binciki wani gida a Ikoyi Legas, inda aka samu Dalar Amurka miliyan 43.4, da Fan 27,800 na Birtaniya da wasu Naira miliyan 23 (Dala 75,000) a gidan da babu mutane a ciki.