EFCC ta gurfanar da Obiano kan badaƙalar N4bn
Hukumar EFCC ta gurfanar da Obiano ne kan zargin laifuka tara a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.
![EFCC ta gurfanar da Obiano kan badaƙalar N4bn EFCC ta gurfanar da Obiano kan badaƙalar N4bn](https://aminiya.ng/wp-content/uploads/2024/01/WhatsApp-Image-2024-01-24-at-10.19.15.jpeg)
Willie Obiano
An gurfanar da tsohon Gwamnan Anambra, Willie Obiano, a kotu kan zargin almundhanar Naira biliyan hudu.
Hukumar Yaki da Masu Karya Tattalin Arziki ta kasa (EFCC) ta gurfanar da Obiano ne a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke zamanata a Abuja.
Hukumar ta gurfanar da tsohon gwamnan ne kan zargin sa da aikata laifuka tara masu alaka da karkatar da kudaden gwamnati a lokacin da yake gwamna a Anambra.
Willie Obiano dai ya musanta zargin da ake masa a yayin zaman kotun.
Daga nan, Mai Shari’a Inyang Ekwo ya dage sauraron karae zuwa ranar 4 ga watan Maris, 2024.