An gurfanar da Yahaya Bello kan zargin N80bn
Hukuamr EFCC ta gurfanar da tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a safiyar Laraba
Hukuamr Yaki da Masu Karya Tattalin Arzkin (EFCC) ta gurfanar da tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, kan badaƙalar Naira biliyan 80.
A safiyar Laraba EFCC ta gurfanar da Yahaya Bello a Babbar Kotun Tarayya da ke Maitama a Abuja.
An gurfanar da Yahaya Bello ne kasa da awa 24 bayan hukumar ta sanar da kama shi, bayan tsawon lokacin suna wasan buya.
A zaman kotu na baya na ranar 14 ga watan Nuwamba, EFCC ta nemi a dage karar zuwa ranar 27 ga watan Nuwamba.
- Najeriya na asarar Dala biliyan 1.1 a duk shekara saboda zazzabin cizon sauro
- Farashin fetur zai sauko a Nijeriya —’Yan kasuwa
EFCC, ta ce wa’adin kwana 30 na sammaci da aka bayar na nan bai kare ba.
Idan ba a manta ba Yahaya Bello, ya shiga wasan buya tsakaninsa da EFCC tun bayan da ya sauka daga mulki.
Duk da zarge-zargen da EFCC ke masa na karkatar da kuɗaɗe a lokacin da yake mulkin Jihar Kogi, Bello ya musanta aikata hakan.